Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Joan Laporta, ya yi karin haske kan dalilan da suka tilasta musu bai wa tsohon tauraronsu Lionel Messi damar sauya sheka zuwa PSG.
Wata sanarwa da ya gabatar a wani manema labarai a ranar Litinin, Laporta ya ce matsalolin kudi ne suka dabaibaye kungiyar wanda suka tabbatar ba ta da ikon ci gaba da rike ‘yan wasa masu tsada.
- Sojojin Amurka 6,000 za su taimaka wajen kwaso mutane daga Afghanistan
- Akwai yuwuwar yawan ruwan sama ya hana jirage tashi – NIMET
Ya ce kungiyar yanzu haka na da bashin yuro biliyan 1 da miliyan 35 a kanta yayin da take biyan albashin yuro miliyan 617 ga ‘yan wasanta karin akalla kashi 25 zuwa 30 idan aka kwatanta da takwarorinta na La Liga.
A cewar Laporta, tsawon shekaru 2 Barcelona na iyakar kokarinta don magance matsalolin kudin da suka dabaibayeta da nufin rike ‘yan wasanta baya ga sayo wasu amma lamarin ya ci tura.
Laporta ya ce zai fi so ya ci gaba da ganin Lionel Messi a tare da su amma ba su da tsimi ko dabarar da ta wuce bashi damar tafiya duk da rashin fahimtar da kungiyar ta samu da PSG a kokarin sauya shekar.
A watan nan ne Messi ya raba gari da Barcelona bayan ta gaza kulla sabon kwantaragi da shi sakamakon wasu dalilai ciki har da batun dokar La Liga da ke kayyade kudin da ya dace kungiyoyi su rika kashewa.
Ana kallon Messi a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da aka gani a tarihin duniya, abin da ya sa sauya shekarsa ta dauki hankalin duniyar wasanni.
Lionel Messi dai ya bar Barcelona bayan shafe shekara 21 yana murza leda a kungiyar.