Ana buga littattafai da jaridun Hausa ta hanyoyin rubutu iri guda biyu. Amma fa, hanyar boko ta rinjayi hanyar Ajami a halin yanzu. Me ya sa haka? Ko saboda boko na ilimin zamani ne? Ko saboda wata babbar kullalliyar Mishan ce?
Wannan babbar matsala ce a tarihin harshen Hausa. Akwai maganganu daban-daban a kan matsalar, amma saboda binciken da aka yi a gidan adana takardun tarihi a Kaduna, a jaridar nan da kake edita za ka ga labari na hakika.
A lokacin da Turawa suka zo nan Najeriya, Hausawa sun yi rubuce-rubuce a harshensu tuntuni. Wasu malamai, musamman danmarina na Katsina, sun yi amfani da haruffan Larabci don rubuta wakokin Hausa, har suka kirkiri wasu sababbin bakake, kamar su tsa don rubutun Hausa daidai wa daida.
Kafin zuwan Turawa, ana amfani da harshen Larabci don aikin hukuma da rubuta wasiku a kasashen Afirka ta Yamma. Hausawa suna rubutun wakokin da harshensu da hanyar Ajami. Wasu ’yan Mishan da masu ilImin harsuna, su kuma suna yin kokarin su rubuta Hausa a boko. Amma ba su daidaita ba a kan yadda za a rubuta sautin Hausa da bakaken boko. Duk da cewa, ko Hausawan ma ba su daidaita a kan yadda ba su rubuta sautin Hausa a bakaken Ajami ba. Har yanzu ana rubuta ‘tha’ a Kananci, amma ana rubuta shin (mai digo a karkashi] a Sakkwatanci (don “c” a boko).
Ko a farkon karni na ashirin akwai ’yan Mishan, wadanda suka fi son rubutu da (Hausa) Ajami. Misali, Malam Robinson, wanda ya wallafa kamus na Hausa da Turanci, a lokacinsu yana yabon Ajami kuma ya buga wakokin Ajami da sharhi a kansu, a Ingila.
Da Gwamna Lugard ya ci kasashen Hausawa da makwabtansu sai ya ba su sunan “Najeriya ta Arewa.” Saboda ka’idojin mulkin mallaka, ya ki ya bar Hausawa su ji abin da shi da wakilansa ’yan Ingila suke cewa a Ingilishi, kada su gane abin da Turawa suke nufi. Kuma wani Bature ya gano cewa dalilin da ya sa Magajin Keffi ya kashe Kyaftin Moloney shi ne, saboda karyar da tafintar Moloney ya yi ne.
An yi bincike, an tabbatar cewa mafi yawan tafintoci kodai su ne barayi ko suna cinikin bayi ko suna cin hanci. ’Yan Afirka, wadanda suka ci amanar ’yan Afirka, ba su rikon amanar Turawa.
To, shi ke nan, sai Gwamna Lugard ya yi fushi da tafintocin, ya ba da oda cewa dole kowane Bature, wanda yake aikin Gwamnatin Najeriya ta Arewa, ya koyi harshen Hausa. Daga wannan oda ta 1902, aka fara manufar nan “Ba Hausa, ba aiki” a Najeriya ta Arewa. Wato in ba ka iya Hausa ba, ba za a ba ka aikin gwamnati ba. An nada farfesan harshen Hausa a Jami’ar Landan, don ya koya wa Turawan Gwamnatin Najeriya ta Arewa harshen Hausa. Amma gwamnati ba ta yanke shawara cewa wace hanya za a bi a yi rubutun harshen Hausa don aikin gwamnati ba tukuna.
Akwai Razdan a Sakkwato mai suna John Alder Burdon, wanda ya goyi bayan Ajami. Ya fadi cewa, tunda ba za a fitar da Ajami daga Adabin Hausa ba, ya kamata a yi amfani da shi a aikin gwamnati, kada a sha wahalar gina sababbin makarantun boko a ko’ina.
Ko dan Mishan din nan na Zariya mai suna Dokta Miller, ya yi rubutu da Hausar Ajami. Ya aika wa Gwamna Lugard da fassarar dokokin gwamnati a Ajami. Miller da Robinson sun rika rubutun (Hausar) Ajami har wasu Turawan Gwamnati, misali Kyaftin Moloney, suna tsammani cewa Ajami ba rubutun Hausawa ba ne na ’yan Mishan ne kadai.
Amma Gwamna Lugard bai saurari wannan nasiha ba. Gwamna Lugard ya ki Ajami. Ya tsaryar da shawarar za a yi amfani da boko a aikin Gwamnatin Najeriya ta Arewa.
Wani dan Mishan mai suna Macintyre, ya rudi Gwamna Lugard, ya gaya masa cewa Hausawa ba su iya karatun Larabci ba, har ya ce Ajami ba bakaken Larabcin gaskiya ne ba. Ya aika wa Gwamna Lugard da wasika a Larabcin Afirka ta Yamma, ya gaya masa cewa shi ne Ajami, kuma ya gaya masa cewa Ajami ba rubutun Hausa ta hanyar Larabci ba ne, har Lugard yana tsammanin Ajami wata hanyar rubutu ce daban ke nan. Macintyre ya gaya wa Lugard cewa Ajami hanyar rubutu wofaye ne domin babu azanci a ciki. kwarai da gaske, mutumin ya yi babbar karya, amma Gwamna Lugard bai sani ba. Bai ji Hausa ba, balle Ajami ko Larabci.
Gwamna Lugard bai gane abubuwan da mutanen suka fada ba. Shi bai fahimci bambanci tsakanin harshe da hanyar rubutunsa ba, har ya ce in ana amfani da boko, Turawa masu aikin gwamnati dole su koyi harshe guda daya, amma in ana amfani da Ajami, dole su koyi harshe guda biyu. Duk da duhun kansa game da harsuna da hanyoyin rubutunsu, shi ne Gwamna, shi zai kafa odoji a Najeriya ta Arewa. Duk da yake shi ba masanin harshen Hausa ba ne, shi ya yanke shawara a kan hanyar rubutun Hausa. Duk da shi ba malami ba ne, balle malamin ilimin koyarwa, shi ya ba da odar yadda za a rubuta harshen Hausa don aikin gwamnati da makarantun zamani a Najeriya ta Arewa.
In an dubi abubuwan da ya ajiye a fayil a Kaduna, za a tabbatar cewa bai fahimci fa’idar amfanin Ajami ba. kwarai da gaskiya bai fahimci hanyar rubutun Ajami ba, balle tarihinsa. Amma ya ki bakaken Larabci har ya aika wa kasar Sudan da wasika, inda ya tambayi ko ana buga littattafan Larabci a boko? Babu wata amsa daga Sudan a fayil a Kaduna.
Duk da haka, da Gwamna Lugard ya koma Ingila don hutunsa a 1903, sai wakilinsa William Wallace ya ba da oda a ranar 12 ga watan Satumba cewa dole a soma rubutun wasika a Hausa. Babu masu ilmin boko a Nijeriya ta Arewa da yawa a lokacin. Saboda odar, an daina karbar wasikun Larabci a gidan Gwamna. Wallace ya ce sai aka fara karbar wasiku a (Hausar) Ajami.
Da Gwamna Lugard ya komo sai ya sa Hans bischer, wato danhausa (wanda gidansa yake Kano har yanzu), ya koyar da boko a wata makaranta a birnin Kano. Hausawa da dama sun shiga makarantarsa. Suna so su fahimci ilimin zamani daga bakin Bature. Da suka gane ba za su koyi Turanci a makarantar ba, balle fasahar zamani sai da yawansu sai suka daina zuwa. Don haka aka ce da makarantar “Makarkata.”
kwarai da gaske, an sha wahala, don ginin makarantun boko. Saboda rashin yawan makarantun, ba yawan masu ilimin boko. Saboda rashin masu ilimin boko, ba masu aikin gwamnati sosai. Saboda rashin ma’aikatan gwamnati, ba kudin haraji sosai a Najeriya ta Arewa. Da Gwamna Lugard ya komo Najeriya sai ya hada Najeriya ta Arewa da ta Kudu a 1914.
Ga mu nan sannu a hankali, Najeriya ta hada kai, Hausar boko ta rinjayi ta Ajami, amma a halin yanzu ba Hausa wadda take harshen gwamnati, sai Ingilishi. Dalili kuwa shi ne, odar da Gwamna Lugard ya ba da.
Dalilin da ya sa rubutun Boko ya tsere wa Ajami a yanzu
Ana buga littattafai da jaridun Hausa ta hanyoyin rubutu iri guda biyu. Amma fa, hanyar boko ta rinjayi hanyar Ajami a halin yanzu. Me ya…