✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa nake wakokin R&B – Mufida Adnan

Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanki? Sunana Mufida Adnan, amma an fi sani da Moofy, an haife ni a Kano, kuma na girma…

Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanki?

Sunana Mufida Adnan, amma an fi sani da Moofy, an haife ni a Kano, kuma na girma a Kano, hakazalika na yi karatu na boko da na Islamiyya a Kano. Ina da difloma a kan harkar lafiya da ake kira Health Information Management; a wannan watan da muke ciki na cika shekara 24.

Aminiya: Me ya ja hankalinki kika shiga harkar waka?

Na fara sha’awar waka ne tun ina karama, idan ba zan manta ba a lokacin ma ban kai shekara 10 ba, akwai dandali mai girma a unguwar da nake, zan iya tunawa muna kiran wurin Dandali Masoya, idan dare ya yi muna zuwa wurin mu yi wasa da kuma rera fitattun wake-waken Hausa, wakokin sun hada da ‘Charmandudu-Charmanduduwa’ da ‘Danfulani na Kiwo’ da sauransu.

Ba zan manta ba ni ce zabiya, ni ce mai fitar da amshi da kuma saka sabuwar wakar da za a shiga. A zahirin gaskiya tun daga wannan lokacin nake sha’awar zama mawakiya, kuma ko lokacin da nake girma sai sha’awar ta ci gaba da karuwa.

Aminiya: Ko kin fuskanci kalubale daga wurin iyayenki da abokanki a lokacin da kika yanke shawarar fara waka?

Gaskiya na fuskanci kalubale mai girma, kada ka manta daga yankin arewacin kasar nan nake, kuma ka san yadda mutanen yankin suke daukar duk wani mawaki, ballantana mawakiya, mutanenmu ba sa daukar waka a matsayin sana’a, inda wadansu kuma suke daukar waka sai namiji ba wai mace ba, ni dai a wurina ina daukar dukkan wadannan abubuwa a matsayin rashin fahimta.

A yanzu duniya sauyawa take, haka zamani ma canzawa yake, don haka abubuwa ma sun sauya, mu ma dole mu sauya hade da daukar sauye-sauyen da za su dace da namu yanayin da al’adar.

A cikin al’ummarmu akwai ’yan ra’ayin rikau da na mazan jiya da suke ganin babu yadda za a yi a samu sauyin al’ada, ina so su sani abin ba haka yake ba, idan ma mun ki yi wadansu da ke jin Hausa za su yi, kuma za a dauke su a matsayin wadanda suke wakilitar Hausawa, a lokacin ne za a yi ta surutu, surutun da kuma babu wani amfani da zai yi mana.

To, ni ma irin yadda ake daukar ba za a samu sauyi a al’adunmu ba ne ya sanya na fuskanci kalubale daga wurin mahaifana, amma sannu-a-hankali na fahimtar da su kyakkyawar manufata dangane da waka, inda hakan ya sa na samu amincewarsu, suka sauko daga hawa dokin naki da suka yi tun a farko. Kuma har yanzu da nake ci gaba da harkar waka ban yi wani abu da mahaifana da kuma abokai da ’yan uwana suka yi tir da shi ba, inda hakan ya ci gaba da ba su karfin gwiwa a kaina.

Aminiya: Masu karatu za su so su ji bangaren da kika fi karkata a harkar waka?

Na fi karkata a bangaren wakokin da Bature ki kira Rhythm and Blues (R&B), kuma ina yinsu da harshen Hausa da kuma Turanci, kuma zan iya cewa mata kalilan ne daga arewa suka dauki wannan bangaren wakar.

Aminiya: A yanzu wane kalubale kike fuskanta a bangaren harkar waka?

Gaskiya ina fuskantar babban kalubale a matsayina ta mawakiya a Arewacin Najeriya, saboda idan mutum bai jajirce ba, to ba zai iya jure tsangwama daga wurin mutanenmu da kuma sauran mawaka maza ba. Kuma ana yi mini wannan tsangwamar ne don kawai a sanya in bar harkar, ni kuwa na tsaya kai da fata, sai na ga abin da ya ture wa Buzu nadi.

Kadan daga irin tsangwamar shi ne, mutum bai san wani shiri kake da shi a kasa ba, haka kawai bai san ka ba sai ka ji ya ce ka bar waka ka yi aure, irin hakan na ba ni mamaki, ka ga mutum ya shiga abin da bai shafe shi ba, kuma idan ka ce ma za ka yi auren, to ya kawo gudunmuwarsa ba za ka sake ganinsa ba, amma ya iya surutu akan abin da ya shafi rayuwarka.

Na biyu, kasancewa a cikin mawaka mata daga arewa da suke wakokin R&B ya sanya ina fuskantar danniya daga wurin mawaka maza, a wadansu lokuta ana cire ni daga manyan tururruka koda kuwa an sanya ni a ciki tun a farko. A gaskiya ina fuskantar kalubale sosai, amma duk da haka bai dakushe ko kashe mini karsashin da nake da shi ba, domin na sani wata rana zai zama labari.

Aminiya: A kwanakin baya kin kai ziyara zuwa Indiya, ko me ya kai ki can din?

Gaskiya ba tafiya ta jin dadi ko hutawa ba ce, a’a, tafiya ce da za ta kasance wani sabon babi a bangaren wakokin R&B a Najeriya gaba daya. Domin ina shirin wakar hadaka da fitattun mawaka a masana’antar wakoki ta Indiya, ina yi wa masoyana albishir din nan ba dadewa ba za su ji wakoki masu ratsa zuciya da kuma sanya nishadi.

Aminiya: A yanzu yaya kike hada kafada da mawaka maza a Najeriya?

Zan iya cewa ina iya bakin kokarina wajen ganin ba a bar ni a baya ba, kuma su ma sun san ina kokari, domin wani ya taba ce mini ina sanya su kara zage damtse. Ni dai abin da ya kawo ni harkar waka shi ne yin wakoki, kuma su din nake yi, kuma sai inda karfina ya kare.

Aminiya: Yawancin mawaka suna daukar cewa idan kana so ka yi suna da kuma kudi sai ka je Legas, shin kina da wannan buri a nan gaba?

Gaskiya ba ni da burin zuwa Legas, domin burina a harkar waka ya wuce Legas, ina da burin zama shahararriyar mawakiya a duniya ne, ka ga kuwa bai zama dole mutum sai ya je Legas ba, domin na ga da yawan mawakan da ba su je Legas ba, amma kuma sun samu daukaka, sun kuma yi kudi, a yanzu zamani ya sauya, abin da ka yi shi ne zai kwace ka a wurin jama’a, shi ne kuma zai sanya ka samu karbuwa ko akasin hakan. Don haka ba zai zama da damuwa ba idan na tsaya a Kano ko na tafi wani wuri, abin da zai haifar mini da daukaka da shahara shi ne idan ina yin wakoki masu kyau da kuma shiga rai, kuma ba ni da wani buri face in yi wakoki masu ma’ana da shiga rai da kuma dadi.

 Aminiya: A kwanakin baya an yi rade-radin cewa an ji muryarki a wata wakar Indiya-Hausa, me za ki ce a kan hakan?

Gaskiya ne, ina daya daga cikin wadanda suke yada fina-finan Indiya-Hausa a Najeriya.

Aminiya: Ko hakan na nufi nan gaba kadan za ki fara fitowa a fina-finai ke nan?

Hakan zai iya kasancewa, amma ina so mutane su sani ko da zan fara fitowa a fina-finai, to ba wai a Kannywood ba.

Aminiya: Wani lokaci kika fi farin ciki a harkar waka?

Lokacin da na fi nishadi da farin ciki shi ne a lokacin da nake gwajin yin wakata ko kuma nake rerawa a dakin daukar wakoki. Hakan na sanya ni jin dadi da kuma nishadi.

Aminiya: Ko kin taba samun lambar girmamawa ko yabo dalilin waka?

Na taba lashe gasar ‘Gwarzuwar Mawakiya bangaren R&B’ na AMMA Awards ta shekarar 2016.

Aminiya: Dangane da batun soyayya fa?

Gaskiya ina da tsayyayen saurayi, kuma kwanan nan zan gayyace ku bikina.

Aminiya: Ko saurayin bai nuna damuwarsa dangane da wakar da kike yi ba?

Ko kadan, sai da na zama mawakiya ma muka hadu, kuma yana ba ni dukkan gudunmuwar da ta kamata ya ba ni a bangaren rayuwar waka.