Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ingila mai suna ‘Three Lions’, Steben Gerrard ya yi ritayar buga wa kasarsa wasa, inda ya ce yawan shekaru da kuma dawowar kulob dinsa na Liberpool buga Gasar Zakarun Turai a matsayin dalilan da suka sanya ya yi ritayar.
Gerrard mai kimanin shekara 34 ya fara buga wa kasarsa wasa ne a lokacin da Ingila ta lallasa kasar Ukraine da ci 2-0 a shekarar 2000, sannan ya buga wasansa na karshe a lokacin da Ingila ta yi kunnen doki 0-0 da kasar Costa Rica yayin gasar cin Kofin Duniya da ya gudana a Brazil.
Ya ce: “Na ji dadin kowane minti da na buga wa kasata wasa, abin bakin ciki ne wannan ritaya, duk da cewa yin ta ne mafi a’ala a gare ni.”
“Na yi ritaya ne saboda yawan shekaru, baya ga haka kulob dina Liberpool ya dawo buga Gasar Zakarun Turai, don haka buga gasar Premier da ta zakarun Turai da ta Kofin FA, sannan na buga wa Ingila wasa akwai wahala.”
Gerrard ya ci kwallaye 21 a cikin wasanni 114 da ya buga wa kasarsa, inda ya kasance dan wasa na uku da ya fi buga wa Ingila wasa bayan Peter Shilton (125) da kuma Dabid Becham (115).
Dalilin da ya sa na yi ritayar buga wa Ingila wasa
Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ingila mai suna ‘Three Lions’, Steben Gerrard ya yi ritayar buga wa kasarsa wasa, inda ya ce yawan shekaru…