✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na kamu da son kasar Maroko – Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Hadiza Gabon ta ziyarci dakin daukar fim na Atlas da ke kasar Maroko, inda ta kashe kwarkwatar idonta bayan ta kalli…

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Hadiza Gabon ta ziyarci dakin daukar fim na Atlas da ke kasar Maroko, inda ta kashe kwarkwatar idonta bayan ta kalli abubuwan tarihi.

Jarumar wanda ta fito a manyan fina-finai irin su ‘Basaja’ da ‘Indon kauye’ da kuma Alkibla’ ta ce ta kamu da son kasar Maroko saboda abubuwan tarihi da kuma dauke kewa da ta ci karo da su a kasar.

“Babu wata kasa da nake matukar kauna kamar kasar Maroko. Na ziyarci dakin daukar fim na Atlas, inda na kalli abubuwan kawa da ado da kuma dauke hankali. Ina fata kasar Maroko za ta ba ni shaidar zama ’yar kasar.

Daga nan jarumar ta halarci kuarzazate, wurin da aka dauki fim din Aladin kashe na biyu, inda ta rubuta, “Idan ka kalli Aladin na biyu, to ka gane wurin da na dauki wannan hoton. Idan mutum yana da rai ba zai daina ganin abin mamaki ba. Na gode wa dakin daukar fim na Ouarzazate Studio.”

Hadiza Gabon ta bayyana cewa Ouarzazate wuri ne na farko da aka fara amfani da shi wajen daukar fim a kasar Maroko, an kuma fara amfani da wurin ne a 1962, inda daraktan kasar Birtaniya Dabid Lean ya shirya fim mai suna ‘Lawrence of Arabia’