✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na jagoranci Kannywood wajen tallata Buhari – Abdul Amart

Abdurrahman Muhammad, wanda aka fi sani da Abdul Amart Mai Kwashewa a Kannywood, fitaccen furodusa ne kuma shi ne Manajin Daraktan Kamfanin Shirya Fina-Finan Hausa…

Abdurrahman Muhammad, wanda aka fi sani da Abdul Amart Mai Kwashewa a Kannywood, fitaccen furodusa ne kuma shi ne Manajin Daraktan Kamfanin Shirya Fina-Finan Hausa na Abnur Entertainment. A hirarsa da Aminiya a makon jiya, ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga harkar fim da burinsa a harkar da kuma dalilin da ya sa ya shiga harkar siyasa gadan-gadan har ya jagoranci Kannywood wajen tallata Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015 da 2019. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Abdurrahman Muhammad, wanda aka fi sani da Abdul Amart Mai Kwashewa. An haife ni a Kano, na yi makarantar firamare ta A’isha Tukur International School da ke Hotoro a Kano, na yi sakandare a Madiya College a Kano, na yi IJMB a College of Arts and Science (CAS), Kano, na yi Professional Diploma a Jami’ar Bayero, (BUK) da ke Kano, inda na karanta aikin jarida  (Mass Communication), na fara digiri a BUK din, sai dai ban kammala ba saboda wasu matsaloli.

Yawanci mutane suna da dalilansu na shiga harkar fim, ta bangarenka mene ne ya ja hankalinka har ka shiga Kannywood?

To, ni dai ma’abocin kallon fim ne da karance-karancen littattafai a baya, tun a farko na dauki fim a matsayin sana’a, na fara harkar ma da zuwa shagon Tukur Hassan da ke Bata a Kano ne, inda nake karbar kaset in sayar, daga nan nake zuwa wurin ’yan fim, sannan idan fim ya fito nakan kalla, daga nan na hadu da antina mai suna A’isha Amart. Ita ta jawo ni ta kai ni lokeshan, sannan ta hada ni da wadansu ’yan fim, daga nan suka dora ni a hanya da kuma yadda harkar fim take, daga nan na fara harkar har zuwa lokacin da na fara shirya fim da kudina. A takaice dai Hajiya Amart ce uwardakina a Kannywood.

Me ya sa ka fi mayar da hankali wajen shirya fim da daukar nauyinsa maimakon zama jarumi kamar yadda yawancin wadanda suka shigo Kannywood suke yi?

A gaskiya da ma ban taba gwada fitowa a fim ba, ni dai mutum ne mai karance-karance, don haka burina in rika kawo labarai ana shirya fim, na shiga harkar fim tun can da burin in rika shirya fim ne, ba wai burin zama jarumi ba.

Zuwa yanzu wace nasara ka samu a Kannywood?

Bayan Hajiya Amart ta raine ni, sai ni da aminina kuma mawaki Nura M. Inuwa muka bude kamfanin shirya fim mai suna Abnur Entertainment, wato Abdul da Nura ke nan, inda muka shirya fina-finai masu yawa. Nasara a cikin hakan kuwa ita ce fina-finanmu sun yi fice, masu kallo sun karbe su sosai, saboda fina-finai ne masu ma’ana da isar da sako.

Zan iya cewa mun shirya fina-finai sun kai 11, fina-finan sun hada da ‘A’isha Humaira’ da ‘Mai Tafiya’ da ‘Ummi’ da ‘Basma’ da ‘Mijin Biza’ da ‘Salma’ da ‘Abbana’ da ‘Afra’ da ‘Yar Amana’ da ‘Wuta Sallau’ da sauransu.

A cikin fina-finan kamfaninku wanne ya fi ba ka wahala wajen shirya shi?

Fina-finai biyu suka fi ba ni wahala wajen shirya su, akwai ‘Mai Tafiya’, saboda sai da muka yi kwana shida kullum muka fita sai an yi ruwan sama, kuma sina-sinan da za mu yi duk a waje ne, ya ba ni wahala sosai.

Sai fim na biyu ‘Mijin Biza’ saboda fim ne da ya shafi jarumai mata da yawa, kowace jaruma da halinta, don haka hada su a wuri daya ya ba mu wahala, kuma a makon da ake daukar fim din sai ya zo daidai da makon bikina, don haka kaina ya dau zafi, amma dai Allah da ikonSa muka kammala daukar fim din.

 Abdul Mart da abokan sana’arsa da Shugaba Buhari da Gwamna El-Rufa’i na Kaduna
Abdul Mart da abokan sana’arsa da Shugaba Buhari da Gwamna El-Rufa’i na Kaduna

A yanzu ana yi maka lakabi da ‘Mai Kwashewa’, yaya ka samu wannan suna?

Na samu sunan ‘Mai Kwashewa’ ne daga wurin ’yan kasuwa, masu sayen fim a wurinmu, Allah da ikonSa tun lokacin da muka bude kamfaninmu na Abnur to duk lokacin da muka yi fim yana samun nasara, kuma ’yan kasuwar da suka saya, suna karuwa sosai, idan na shiga kasuwa ko muka hadu a wani wuri sai ka ji sun ce, ai Alhamdulillah mun kwashe da fim dinka.

Daga nan idan sun gan ni sai su ce ga ‘Mai Kwashewa’, sai in ce ku ne dai kuke kwashewa tunda muna sayar muku da hakkin mallaka. Amma sunan ya watsu sosai ne lokacin da muka yi wakar ‘Lema Ta Yage’ a shekarar 2015 ke nan, inda Adam Zango ya kara kambama sunan a cikin wakar.

A watannin baya an ga ka raja’a sosai a harkar siyasa, kusan ma za a iya cewa kai ne ka hada kan ’yan fim masu son Baba Buhari, ko me ya jawo haka?

Asalina dan siyasa ne, kakana dan siyasa ne, wato marigayi, Alhaji Abubakar Dzukoji, mutanen NEPU ne, ya yi siyasa da Aminu Kano, kusan ma zan iya cewa siyasa ce ta sanya kakannina suka bar Jihar Neja suka dawo Kano, har aka haife mu a nan Kano. Kakana ya yi Ma’ajin Kudi na Jam’iyyar NEPU ma. Don haka siyasa a jinina take, kuma na fara tun kafin in shiga Kannywood.

Ni masoyin Baba Buhari ne, na fara bin Buhari tun daga APP zuwa CPC har zuwa APC, kuma tun a shekarar 2015 na rika yi wa Baba Buhari kamfe. Ni na shirya wakar ‘Lema Ta Yage’ ma da kudina, babu tallafin kowa, duk saboda son Baba Buhari. Don haka a zaben 2019 ma sai na ce ai ni masoyin Baba Buhari ne, kuma ina da damar ba da gudunmawata ta yi masa kamfe, ga shi kuma na yi karfi a cikin sana’ata. Sai na ce bari in taimaka wa Baba Buhari, hakan ya sa na jawo wadanda suke da ra’ayinsa cikin tafiyar, sannan muka yi kamfe, kuma mun yi kokari wajen yadda muka shawo kan wadansu mutane a Kannywood da ma wadanda ba ’yan Kannywood ba, inda aka samu nasara kuma.

Shin ka gabatar wa Baba Buhari wasu kudirorin Kannywood da kuke so ya yi muku a yanzu da aka samu nasarar cin zaben 2019?

Tunda ake siyasa a Kannywood, zan iya daga hannu babu wadanda suka kai kudirorinsu kafin su fara talla kamar tafiyata, saboda mun yi magana a kan masana’antarmu, kuma ka san mun yi tallar Buhari tun wancan tafiyar, kuma babu abin da gwamnati ta yi wa masana’antarmu. Kafin mu fara wannan tallar da kuma kamfe sai da muka kai kudirorinmu, kuma ta silar wanda ya taimaka mini a wannan tafiyar Alhaji Musa Halilu, Dujiman Adamawa, na samu nasarar jawo ’yan fim masu yawa cikin tafiyarmu. Kuma mun samu alkawura daga Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya A’isha Buhari da ofishin Baba Buhari.

Kudurorin ma a yanzu suna daf su fara tabbata, ka san dai kasuwar fim ta DBD ta ja baya, to an yi mana alkawuran za a gina mana sinimomi a jihohi, sannan za a samar mana da wata kafa da za mu rika kasuwancin fina-finanmu. Ga batun ba da tallafin jari da sauransu.

Ga shi kana siyasa gadan-gadan, to ko nan gaba kana da burin fitowa takara?

Kusan duk wanda ya san Abdul Amart, ya san mutum ne mai fadar gaskiya, don haka ba ni da burin in fito takara saboda ni mutum ne da ba na karya. Siyasa kuma sai da kwane-kwane, ni kuma ban iya haka ba, wannan dalili ne ya sa nake ganin kamar ba zan iya fitowa takara ba.

Yawancin furodusoshi suna da jaruman da suka fi jin dadin aiki da su, saboda wasu dalilai, a naka bangaren wadanne jarumai ka fi jin dadin aiki da su?

A cikin jaruman da na fi jin dadin aiki da su babu sama da A’isha Aliyu Tsamiya, saboda idan ma ka kalli fina-finan Abnur za ka ga duk kusan ita ce a ciki, saboda ina jin dadin aiki da ita, ta iya aiki, kuma labaran da muke yi ita suka fi kira. Tana ba mu abin da muke so, sannan ba ta da korafe-korafe irin na wadansu jarumai.

Mene ne babban burinka a Kannywood?

Babban burina shi ne a yanzu ina da fina-finan da nake so in yi wadanda suka shafi abubuwan da suke ci mana tuwo a kwarya, musamman a kan miyagun ayyuka, misali, a farko duk da na yi fim din ‘Dan Almajiri’ a baya, to dole sai na sake yin fim a kan almajirci, mece ce silarsa da kuma hanyar da za a magance shi? Sannan mata a Arewa sun lalace da shaye-shayen miyagun kwayoyi, zan yi fim a kan wannan matsala, ga matsalar fyade da sauransu. Hakan ne ma ya sa na zo da fim mai taken ‘Manyan Mata,’ shiri ne da dole sai gwamnati ta tallafa, ku san ma zan ce al’amarin ya yi nisa ta bangaren tallafin gwamnati.

Sannan ina da burin Kannywood ta samu ci gaba kamar yadda takwararta ta Kudancin kasar nan ta samu, hakan ne ma ya sa na kara dagewa wajen tallata Baba Buhari.

Ka yi wa APC da Baba Buhari hidima, idan aka kai ga ba ka wani mukami za ka karba? Idan za ka karba, shin ta yaya za ka taimaka wa Kannywood wajen ganin ta samu ci gaba?

Ku san dai duk wadanda muka yi tafiyar Kannywood ta APC da su, ko rawar da na taka ta wajen tattara ’yan fim da kuma yadda muka kamanta adalci a tafiyarmu kusan idan suka ji za a ba ni wani mukami, to za su yi murna. Domin sun samu wanda yake kishinsu, kuma akalla zan yi kokari wajen kawo musu ci gaba. Don haka ba ni da wurin da ya fi Kannywood ko an ba ni mukami na kammala dole Kannywood zan dawo, don haka zan taka rawar da Kannywood za ta samu ci gaba da daukaka matukar aka ba ni mukami.