Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanki.
Maryam Abubakar: Ni dai sunana Maryam Abubakar, kuma ni haifaffiyar garin Legas ce, a yanzu ina da shekaru 20 a duniya, kuma na yi makarantar firamare da sakandire duk a garin Legas. Daga nan dai ban ci gaba ba sai dai nan gaba nake so in ci gaba da karatun.
Aminiya: Ko kin taba yin fim a rayuwarki?
Maryam: To, gaskiya dai ina sha’awar shiga harkar fim, amma dai ban samu shiga ba sai da aka zo tantance jaruman da za su fita a cikin fim din ‘Bilkisu’ sai ni ma na shiga, kuma Allah Ya sa na samu nasarar zama jarumar fim din.
Aminiya: Yaya kika ji a lokacin da aka sanar cewa ke ce kika yi nasarar a wajen zama jarumar da za ta jagorancin fim din ‘Bilkisu?
Maryam: To, gaskiya na ji dadi sosai, don kuwa abin da na dade ina nema ne, sai kuma na samu, don haka tun kafin a fara fim din, mutane da dama suka rika taya ni murnar samun nasarar da na yi.
Aminiya: Ganin cewa shi ne fim din ki na farko, ko yaya kika samu kanki a daidai lokacin da za a fara aikin daukar fim din?
Maryam: To, gaskiya abin da sauki kuma ba sauki, saukinsa shi ne ina da sha’awar harkar, rashin saukinsa kuma shi ne yadda zan bullo wa harkar da ban taba yi ba. Hakan ya sa na samu kaina a cikin wani irin yanayi.
Aminiya: Da yake labarin da kike samu na aikin fim ana yin kwana biyar zuwa goma a kammala, to ke kuma ga shi a tashin farko kin samu kanki a fim din da kika shafe kusan wata biyu ana yin aikinsa, to yaya kika iya jure tsawon lokacin a lokeshin?
Maryam: To, gaskiya wannan abin ba mai sauki ba ne, domin kuwa shi aiki irin wannan aiki ne da tun kana marmarinsa, to sai ka zo ka gaji da shi har ka matsu a gama, amma dai da yake ina da burin abin a zuciyata, hakan ya sa na samu dakewa wajen gudanar da aikin.
Kuma gaskiya a ranar farko na fi shan wuya, ba kamar lokacin da aka ce na yi rol din kuka na samu dai na yi, amma sai da ya zama kamar ba zan iya ba saboda wahala.
Aminiya: Ganin an shafe tsawon lokaci ana daukar fim din, ko me ya fi burge ki, wanda hakan ya sa kike samun kwarin gwiwar ci gaba da harkar fim?
Maryam: To ni ina samun kwarin gwiwar idan na ga na yi rol din da aka ba ni, kuma daraktan fim din ya yaba kwazona, don haka sai na samu kwarin gwiwar yin na gaba.
Aminiya: Duk jarumar da ta shiga harkar fim ta fi so ta taka wani rol na soyayya, to sai ya zamo kin samu kanki a fim mai dogon zango, kuma ba na soyayya ba, ya kika ji da hakan?
Maryam: E, to, haka ne, amma dai duk da fim din ‘Bilkisu’ ba na soyayya ba ne, irin darasin da yake cikinsa zai sa idan fim din ya kammala in aka kalle shi in samu daukaka, da man dai ana so a san mutum ne, kuma shi fim din ba ma wanda za a sayar da shi a kasuwa ba ne, za a haska shi ne a manyan gidajen talabijin na duniya.
Aminiya: Me kika dauki fim din ‘Bilkisu’ a rayuwarki?
Maryam: To, ni ina ganin fim din ‘Bilkisu’ shi ne sirrin nasarar rayuwata. Don kuwa a matsayinsa na fim dina na farko sai ya zama ya kai ni matsayin babbar jaruma ta duniya, don na fada maka ba fim ne da za a sayar a kasuwa ba, fim ne da duk duniya za a gan shi, kuma Alhamdulillahi ina alfahari da wannan nasara da na samu.
Aminiya: Idan na fahimce ki, fim din ‘Bilkisu’ ya ba ki damar nan gaba za ki iya shiga kowanne irin fim?
Maryam: Wannan haka yake, da ma kwarewa ake bukata, kuma ina ganin duk abin da ka sa a gaba kana yin sa yau da kullum ka shafe kusan wata biyu ai ka samu kwarewa.
Aminiya: Yanzu mene ne burinki na gaba?
Maryam: To burina dai shi ne, Allah Ya kara daukaka ni, in rika samun nasara a harkar rayuwata.
Aminiya: Wanne sako kike da shi?
Maryam: To sakona dai shi ne godiya ga shi wannan kamfani na Amara wanda shi ne ya shirya fim din, kuma ta hanyarsa ne na samu wannan dama, kuma ina godiya ga shi daraktan fim din, wato Balarabe Murtala Baharu da ya tsaya tsayin daka don ganin na samar da abin da ake so a cikin fim din.