✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na canja sunan masarautata – Oluwo na Iwo

Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi ya ce, mutanen da ba sa son kyautata canjin zamantakewar kabilu da ci gaban kasa sne suke sukar matakin…

Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi ya ce, mutanen da ba sa son kyautata canjin zamantakewar kabilu da ci gaban kasa sne suke sukar matakin da ya dauka a ranar Asabar da ta wuce na canja sunan sarautarsa daga Oba zuwa Amir (Emir -Sarki) a kasar Yarbawa tare da nadin da ya yi wa Sheikh Yakub Abdul-Baki Muhammed a matsayin Wazirin Iwo. 

Da yake yi wa dimbin jama’ar da suka halarci fadarsa bayani ya ce ya dauki matakin ne saboda yana so ya yi koyi da Sarakunan Hausawan Arewacin kasa da suke yin taro a kai -a kai domin tattauna matsalolin da suka shafi jama’arsu da kasa baki daya, inda ya ce Sarakunan Yarbawa ba sa yin haka a sashen Kudu maso Yamma saboda gabar da ke tsakaninsu.

Wadansu kungiyoyin Yarbawa sun nuna rashin jin dadinsu kan daukar wannan mataki da Oluwo na Iwo ya yi inda suka yi zargin cewa da hannun wadansu sarakunan Arewa a kan bayanai da matakan da Oluwo ke dauka inda suke ganin zai iya haifar da hatsaniya a Najeriya.

Hakan ne ya sa Oluwo ya canja kalaman da ya yi bayan kwana biyu da fadin kalamansa na farko, inda a ranar Litinin da ta wuce Oluwon ya ce ba zai yi watsi da sunan Oba da ake kiran sarakunan Yarbawa da shi kaka da kakanni a masarauta ta Iwo da kasar Yarbawa ba.

Ya fadi haka ne a jawabin da ya yi ga taron kungiyar Teloli da suka kai masa ziyarar ban girma da kuma mabiya addinin Kirista da suka shirya addu’ar Ista a fadarsa da ke garin Iwo a Jihar Osun. A matsayinsa na Musulmi Sarkin ya  taka rawa da yin wakokin mabiya addinan biyu a gaban jama’a, ya ce al’ummar Hausawan da suke zaune a masarautarsa suna kiransa da sunan Emir (Sarki) ne kamar yadda suke kiran sarakunansu na Arewa. Haka kuma kabilun Ibo suna kiransa da sunan Eze.

“Saboda haka zan ci gaba da yin amfani da sunan Emir da Eze da Attah domin duk ma’anarsu daya ce wato Sarki kuma zan ci gaba da yin amfani da sunan Oba da muka yi gado kaka-da-kakanni.” Ya ce bai ga dalilin sukar matakin da ya dauka ba domin “A matsayina na Sarki kuma shugaban wadannan al’umma da ke zaune a masarautar Iwo yana da kyau in bullo da sabuwar hanyar dinke barakar da ake samu ta kyamar juna a tsakanin kabilun Najeriya.”

Ya ce ya kamata a daina kyamar kabilun da suke zaune a jihohin da ba nasu ba. “Ya kamata kowane dan kasa ya ci moriyar ’yancin kai da zamantakewar da za ta ba shi damar zama dan takarar kujerun majalisun dokokin a kowace jihar da yake zaune a matsayin bako. Wannan shi ne burin da nake so a samu canjin da zai fara daga kawunan sarakuna.”

“Hassada da rashin fahimta ce ta sa ake sukar wannan mataki da na bullo da shidomin samun hadin kan al’umma da dorewar dunkulalliyar Najeriya” inji Oluwo na Iwo.