Wata jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Sanata Baraka Sani ta kaddamar da gidan talabijin na intanet mai suna ‘Atiku TV’ da zai rika tallata manufofin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Ta ce an bude tashar ne domin yada manufofi da akidun Atiku wanda ta bayyana a matsayin wata babbar kadara ga Najeriya wanda ya kamata a adana gudunmawarsa domin amfanin ’yan baya.
Sanata Baraka wacce tsohuwar babbar mai taimaka wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ce kan harkokin noma ta ce sabuwar tashar ba ta da alaka da wata manufa ta siyasa ko takarar Atikun a shekara ta 2023.
“Wannan tashar ba ta tallata takarar Atiku ba ce a 2023; Ya wuce haka matuka.
“Mun bude ta ne domin yada manufofinsa na siyasa da za su taimaka wa matasa da suke tasowa su samu kwarewa a siyasance; akwai abubuwa da yawa da za su koya daga hikimomi da fasaharsa,” inji ta.
Shawarar bude tashar, a cewarta, ta biyo nazari da suka yi tare da gano cewa sama da mutum miliyan 130 ne ke amfani da kafafen sada zumunta, wadanda mafi yawansu matasa ne.
Matasa su ne rabin masu zabe a Najeriya wanda ya zama wajibi a yi amfani da kafar da ta dace muddin ana so a samu amincewarsu, inji ta.
“A cikin lamarin Atiku, akwai babban darasi da mutanen Najeriya za su koya.
“Za su fahimci cewa rayuwa ba ta bukatar karaya, ta fi bukatar jajircewa da fadi-tashi ko bayan yin rashin nasara matukar dai kana da wata gudunmawa da za ka ba jama’a.
“Atiku ya tara kusan dukkannin abun da siyasar Najeriya ke bukata,” inji ta.
Shi kuwa tsohon mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, cewa ya yi bude tashar ya zo a lokacin da ake bukata, domin zai taimaka wajen kawo karshen siyasar ta’addanci a Najeriya.
“Idan ka je Amurka da sauran kasashen Turai yanzu haka duk yakin neman zabensu ya koma kafafen yada labarai. Lokaci ya wuce da ’yan siyasa za su rika tara gangami ko su debo ’yan daba.
“Kawai abun da ake bukata shi ne ka shaida wa mutane abun da ka tanadar musu”, inji Sanata Gwarzo.