✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa muke yin amfani da masana na gida don bunkasa al’umma – NCC

Shugaban Hukumar Sadarwa na NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya ce hukumar ta himmatu wajen yin amfani da masana ta hanyar gudanar da bincike da…

Shugaban Hukumar Sadarwa na NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya ce hukumar ta himmatu wajen yin amfani da masana ta hanyar gudanar da bincike da kirkira don bunkasa hada-hadar kasuwanci da al’umma.

Farfesa Danbatta ya bayyana haka a Abuja yayin da yake kaddamar da kwamitin shiga tsakanin ma’aikatu don tantance binciken da masana suka gabatar na shekarar 2018.

Ya ce Hukumar ta himmatu wajen wannan kuduri saboda  yin amfani da mafitar da masanan na gida suka bayar ga kalubalen da masana’antar ke fuskanta shi ne tsarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ke mutukar so.

Ya bayyana cewa kaddamar da kwamitin ya zama wajibi ga masana’antar sadarwa kuma abu ne mai mutukar amfani ga gungun masana ta hanyar sanyawa kwalliya ta biya kudin sabulu ga binciken da aka fitar.

‘Burinmu shi ne mu yi amfani da fasahar masana na gida tare da yin amfani da ita wajen sanya ta cikin tsarin bincike don ya yi tasiri ga kasuwanci da al’umma don bunkasa sabuwar haja da ayyuka a masana’antar baki daya. Mun amince cewa a matsayin masana’antar wacce take da kima a duniya kuma ta bayar da gudunmawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa, bangaren zai iya fadada ilimin masana tare da amfana daga gudunmawarsu’’. Inji shi.