Kungiyar Boko Haram tsagin da Abubakar Shekau ta dauki alhakin kashe manoman shinkafa da aka yi wa yankan rago a kauyen Kwashebe da ke yankin Zabarmari na Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.
Abubakar Shekau a wani sabon bidiyo na tsawon minti uku da ya fitar a ranar Talata, ya ce su ne suka kashe manoma 78 sabanin 43 da kafafen yada labarai da dama suka yada.
- Dalilin da ya sa Kotu ta kawo karshen shari’ar Naziru Sarkin Waka
- Yadda aka ceto mata 4 masu ciki a gidan sayar da jarirai
- Dalilin da ya sa Kotu ta kawo karshen shari’ar Naziru Sarkin Waka
Shekau, ya ce sun kashe manoman ne saboda mutanen kauyen Zambarmari sun kama daya daga cikin mutanensa kuma suka mika shi a hannun sojojin Najeriya.
A bidiyon, Shekau ya ce, “Muna gargadin duk wani mutum da ke shirin kama daya daga cikin ’yan kungiyarmu ya mika wa jami’an tsaro ko ya fallasa ayyukanmu ga Rundunar Sojoji, to shi ma zai fuskanci makamancin hukuncin da wadannan manoman suka fuskanta idan ba a kiyaye ba.
Sabani kan adadin mutanen da aka kashe
An samu sabanin kan hakikanin adadin mutanen da aka kashe tun lokacin da rahoton kisan gillar da aka yi wa manoman ya bulla.
Tun da fari an samu rahotanni daga kafafen yada labarai daban-daban cewa mutum 43 kungiyar ta kashe a Zabarmari.
Daga bisani kuma Babban Jami’i a Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, Edward Kallon, ya fitar da rahoton cewa mutum 110 aka kashe sabanin rahoton da rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa mutane 43 ne suka mutu a harin da aka kai wa manoman.
A ranar Lahadi ne Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya halarci jana’iza tare da fadi-tashin binne mamatan da mayakan Boko Haram suka kashe.
Aminiya ta rawaito cewa, mutanen da abun ya ritsa da su, manoman shinkafa ne wanda aka kai musu hari lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu da ke yankin Koshebe, inda aka yi musu kisan gilla ta hanyar yankan rago.