Shugaban kungiyar mata masu sayar da abinci a Jihar Katsina, Hajiya Furera Ibrahim ta bayyana burinsu na bunkasa tattalin arzikin kasar ne ya sanya suka kafa kungiyarsu.
Ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da wakilin Aminiya a Katsina a ranar Litinin.
Shugabar ta ja hankalin ’yan kungiyar don su ci gaba da bada hadin kai don kungiyar ta bunkasa.
Ta ce: “Kowace irin sana’a ana kafa mata kungiya, sai na ga mu masu sana’ar sayar da abinci ana neman a bar mu baya, bayan kuma mu ne suka kamata a ce ke kan gaba. Ko mutum bakunta ya je a garin da bai san kowa ba, mu yake fara nema, kuma mu ke fara karbar bakuncinsa. Kuma sana’ar sayar da abinci babu inda babu ita a duk fadin duniyar nan, amma sai ya zamo muke zaune kara zube, babu hadin kai a tsakaninmu, ballantana mu ciyar da kasuwancin gaba.”
Ta jaddada za su taimaki junansu ta hanyar kungiyar da suka kafa, inda a yanzu za su iya magana da murya daya.
“Ta hanyar kungiya za mu iya sanin junanmu da kuma yin magana da murya daya. Za mu rika taimaka wa juna ta hanyar tallafi, kamar jari ga wadanda kasuwa ta yi wa halinta bayan mun yi bincike.”
Ta tabbatar za su bayar da gudunmuwa bunkasa tattalin arziki a Jihar Katsina.
“Zaman mu na mata mun san akwai gudunmuwar ci gaba da za mu bayarwa, domin kowane lungu ka shiga za ka samu masu sayar da abinci.” Inji shugabar.
kungiyar ta shekara daya da kafuwa inji shugabarta, ta kuma taimaka wa mata masu sayar da abinci bakin gwargwado ta fuskoki da dama.