Shugaban kwamitin tsare-tsare na filin wasan Freedom Theater da ke unguwar Agumalu a yankin Apapa a Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Akashe ya ce zuwan azumin watan Ramadan da kuma gyaran filin wasa ne suka sanya aka dakatar da wasan kokawa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya ta wayar salula a karshen makon da ya gabata.
Ya ce: “Ka san yanzu muna cikin azumi kuma mu dama idan azumi ya zo muna dakatar da wasannin da muke yi a gidan dirama. Daga cikin wasannin da muka dakatar har da wasan kokawa da na kade-kade da raye-raye. Kuma shi filin da ake yin kokawar muna yi masa gyara saboda ruwan da yake zama a wurin. Tuni an zuba yashi don tabbatar da jin dadin ’yan wasan da kuma ’yan kallo ta yadda jama’a za su more kudin da suka biya yayin shiga gidan wasan’.
Ya ce idan Allah Ya yarda bayan karamar sallah za su dawo da shirye-shirye masu kayatarwa da debe kewa.
Ya ce sun gayyato ’yan kokawa daga jihohin Jigawa da Kano da Katsina da Sakkwato har ma da kasar Nijar kamar su Gogau da shago da karago da su dan Ibo da shagon Lawalli da sauransu.
‘Dalilin da ya sa muka dakatar da wasan kokawa a Legas’
Shugaban kwamitin tsare-tsare na filin wasan Freedom Theater da ke unguwar Agumalu a yankin Apapa a Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Akashe ya ce zuwan azumin…