Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta bayyana dalilan da ya sa ta dakatar da aikin gina jami’a a yankin Rigachikun da ke Jihar Kaduna a matsayin rashin cika sharrudan girman fili da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta gitta.
Shugaban Kungiyar ta Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da masaukin baki mai hawa biyu da kungiyar ta gina a Unguwar Life Camp da ke Abuja.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce filin da aka tsara gina jami’ar na da girman hekta 7 ne sabanin hekta 100 da Hukumar NUC take bukata don daukar dukan tsangayoyi da jami’a za ta koyar. Ya ce sakamakon haka kungiyar ta yanke shawarar amfani da filin na Rigachikun don ba da horo a kan sana’o’i ga jama’a a yayin da take shirin yin jami’ar a wurare uku da wasu gwamnonin jihohin Arewa suka yi mata alkawarin samarwa a jihohinsu mai girman hekta dari-dari.
Daraktan ’Yan agaji na Kungiyar Injiniya Mustafa Imam Sitti wanda ya zanta da Aminiya bayan taron ya ce kungiyar Izala ta yanke shawarar gina masaukin bakin ne don samar wa malamai da sauran bakinta da take gayyata masauki a Birnin Tarayya don gudanar da wa’azuzzuka da sauran ayyukan addini musamman a tashoshinta na talabijin da rediyo na Manara, maimakon kama musu masauki a otel-otel na ’yan kasuwa da hakan ke cin makudan kudi, kuma malaman ke cakuduwa da maziyarta otel-otel din da suke ayyukan masha’a a wasu lokuta.
Sakataren Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Muhammad Kabir Gombe da Mai martaba Sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa wanda ya wakilci Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Malam Muhammad Musa Bello a wajen taron, sun jagoranci neman taimako don aikin gina sakatariyar kungiyar tare da masallaci. Taron ya samu halartar manyan baki da sauran jama’a daga sassan kasar nan.