✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista

Ministan ya ce gwamnan ya zagi mahaifinsa wanda hakan ya sa ya fusata.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara jihar.

A watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya mari Minista Tuggar a cikin mota yayin da suke kan hanyar zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi.

Amma Mataimakin Gwamnan ya musanta faruwar hakan.

Da yake zantawa da BBC Hausa, Tuggar ya ce saɓanin ya samo asali daga wajen Gwamna Bala Mohammed ba daga wajen mataimakinsa ba.

“Muna cikin mota tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa,” in ji Tuggar.

“Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi magana da ni, sai Gwamna Bala, wanda ke zaune kusa da shi, ya tsoma baki a zancen da bai shafe shi ba, ya kuma fara zagin mahaifina, wanda ya rasu sama da shekaru 20 da suka wuce. Daga nan sai ya ce zai mari ni.”

Tuggar ya ce ya tashi tsaye domin nuna cewa ba zai lamunci cin zarafi ba.

“Na tashi tsaye domin na nuna masa cewa ba zai iya cin galaba a kaina ba. Sai Mataimakin Gwamnan ya taho daga baya yana cewa shi ma zai mari ni.

“Amma bai samu damar ƙarasowa waje na ba, saboda Mataimakin Shugaban Ƙasa na cikin motar,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa ba a yi faɗa da su ba, sai dai barazanar mari.

Ya kuma zargi ɗan Gwamna Bala da yaɗa labaran ƙarya a Intanet.

“Ɗan Gwamnan ya fito a shafin sada zumunta yana cewa an mari ni, wanda ba gaskiya ba ne. Ko Mataimakin Gwamnan daga baya ya tabbatar da cewa ba a mari ni ba,” in ji Tuggar.

Tuggar ya ƙaryata zargin da ke cewa saɓanin yana da alaƙa da burinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027.

“Ko da zan tsaya takara ko ba zan tsaya ba, idan lokaci ya faɗin gaskiya ya yi, sai na faɗa. Wannan abu yana shafar ƙaramar hukumarmu da garinmu Udubo,” in ji shi.

Ya danganta saɓanin da yadda ake tafiyar da gwamnati a Bauchi, musamman batun mallakar filayen noma da kiwo.

“Ana ƙwace filayen manoma da makiyaya ana bai wa wasu kamfanoni. Waɗannan kamfanonin suna karɓar bashi suna cewa za su yi noma, amma babu wani ci gaba,” in ji shi.

“Idan da gaske ci gaban jihar ake so, me ya sa Bauchi ba ta zama a gaba ba wajen harkar noma ko kiwon dabbobi ba? Sai ma abin ke ƙara taɓarɓarewa.”

Tuggar da Mataimakin Gwamna Jatau duk daga Yankin Sanatan Bauchi ta Arewa suke, wato yankin da ba a taɓa samun gwamna daga can ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Ko da yake Tuggar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027 ba, alamomi sun nuna yana da sha’awar tsayawa.