✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko

Dalilan da ke hana ’yan mata da suka yi ilimin boko mai zurfi auruwa da wuri.

Binciken Aminiya ya gano abin da ya sa maza da dama ke gudun auren ’yan mata masu zurfin karatun boko, lamarin da ke shafar rayuwar matan kai-tsaye.

Rashin son takura wa rayuwar matan domin su samu damar cin duniyarsu da tsinke, kwarjininsu ga wasu mazan da ke son tunkarar su da bautn aure da tsoron cewa matan za su yi wa maza wuyan sarrafa, kadan ne daga cikin abubuwan da ke kawo rashin auruwar matan masu zurfin karatun boko da wuri.

Yawancin mazan da Aminiya ta tattauna da su sun nuna cewa abin da ke hana su auren matan da suka yi karatu mai zurfi shi ne tsoron da suke da shi na cewa matan ba za su yi saukin sarrafuwa ba.

Suna kuma tunanin matan na da dogon burin ganin sun yi rayuwa cikin daula da alatu na irin manyan gidajen zamani.

Wuyar sha’anin matan—Saurayi

Wani saurayi mai suna Mubarak Muhammad a Kano ya bayyana wa Aminiya cewa yawancin mata masu zurfin karatu na da dogon buri da ke hana maza neman aurensu.

“Za ki samu yawancin matan da suka yi karatun boko mai zurfi suna da dogon buri da son yin rayuwa ta jin dadi wanda kuma ba dukkan maza ke da wadatar yin haka ba.

“Ba ya ga budewar idanu da matan kan samu, za ki samu matan da suka yi karatu mai zurfi suna da gogewa sakamakon cudanya da suka yi da mutane daban-daban a lokacin karatunsu.

“Don haka maza ke tsoron auren su saboda al’adarmu musamman a nan yankinmu na Arewa, namiji bai fiye son auren mace mai budadden ido ba, domin a tunaninsa ba zai iya sarrafa ta yadda yake so ba,” inji shi.

Yawan shekaru

A cewar mutane da dama, yawan shekaru da matan da suka yi karatun boko mai zurfi suke da su sakamakon jan lokaci wajen karatun na janyowa mazan suke kin auren su.

“Zan iya cewa yawan shekaru yana daga cikin kalubalen da ke hana matan samun mijin aure saboda ba za ki hada shekarun matar da ta yi karatu da wacce ba ta yi dogon karatu ba.

“Namiji zai ga cewa don me zai je ya auri macen da ta girme shi ko suke sa’anni?

“Shi a ganinsa ta yi masa tsufa, ya fi son ya auri yarinya mai jini a jika,” inji shi.

Dogon buri da raina maza

Mubarak ya kara da cewa a wasu lokutan ba maza ne irin wadannan matan ba su samu ba, su da kansu ke kin yin auren saboda gurin da suke da shi a rayuwa.

Ya ce, “A wasu lokutan matan sukan samu mazan da ke son su da aure amma sai matan su raina su, saboda karatun da suke ganin sun yi.

“Sai su rika ganin cewa su sun fi karfin auren wannan namiji. A ganinsu ajinsu ya fi nasa da sauransu.”

Tasirin rayuwar turawa

Abdullahi Bashir Muhammad ya bayyana wa Aminiya cewa maza na gudun auren matan da suka yi karatu mai zurfi ne saboda yawancin matan sukan tasirantu da al’adun Turawa.

“Idan matan nan suka zurafafa a karatun boko, za ki samu cewa sun tasirantu da rayuwar Turawa ta fuskar tarbiyya da sutura da harshe da abinci da sauransu, wadanda kuma za ki samu abubuwa ne masu tsada da wuyar samu.

“A waje daya kuma za ka samu tana son yawan fita bukukuwa da dare, kuma duk yayin da mijin ya hana ta, to fa za a iya samun matsala,” inji shi.

Matsalar aikin albashi

Ya ce wani dalilin shi ne yawancin matan da suka yi karatu mai zurfi sukan nuna sha’awar yin aikin albashi ta hanyar cudanya da maza.

Ya ce namiji na iya zargin ta da wani abu idan tana aikin ko kuma ya rika tunanin za ta gagare shi sarrafawa saboda kudin da take samu.

Karancin wayewar maza

Shi kuwa Ahmad Abdullahi ya ce yawanci rashin wayewa ke sanya maza kin auren matan da suka yi ilimin mai zurfi.

“Ni ina ganin akwai karancin wayewa a wajen maza musamman a nan Arewa inda suke kyamar auren masu zurfin karatu.

“Saboda wai suna tunanin matan suna zamantowa masu karancin kunya saboda cudanya da suke yi da maza,” inji shi.

‘Rashin kamun kai’

Sai Abdurrahman Alkassim ya ce ana zargin irin wadannan mata da rashin kamewa shi ya sa maza ke gudun auren su.

“Yawanci za ki samu matan da suka yi karatu mai zurfi ba su damuwa da kamewa a yayin da suke hulda da maza inda wata macen za ka same ta a tsakiyar maza ba tare da nuna ko damuwa ba.

“To ina ganin da za a samu matan su zama suna kamewa a lokacin da suke karatu gaskiya da mazan sun yi rububin auren su a lokacin da suke karatun ko bayan sun kammala ba tare da jin wata fargaba ba,” inji shi.

‘Maza na neman sauki’

Sai dai a bangaren wata budurwa da ke karatu a Jami’ar Bayero mai suna Yahanasu Sani, ta bayyana dalilin a matsayin gudun da mazan ke yi cewa ba za su samu damar cutar matansu ba.

“Ina ganin dallilin bai wuce maza suna son auren wacce za su raina wa hankali ba, su rika wasa da hankalinta.

“Kin san ba za ki hada matar da ta yi karatu da wacce ba ta yi ba.

“To a zamantakewa idan har miji yana son yin wani abu da ba ya son ta gane, zai iya yi mata rainin hankali.

“Amma ita mai ilimi kasancewar ta yi wayo ba za ta yarda da haka ba,” inji ta.

Maza masu kyashi

Ita ma Fatima Hassan ta bayyana cewa mazan suna kin auren mata masu zurfin karatu ne saboda kyashin da suke da shi.

“Namiji saboda son kansa kullum so yake ya ga mace ta dogara da shi duk da kasancewa ba shi da karfin da zai iya daukar nauyinta.

“Amma sai ki ga ki-fadi da kyashi sun sa ya ki ya auri mai karatu don kada ta yi aiki ta zama tana dogaro da kanta,” inji ta.

A cewarta, duk da sun san kaurace wa aurensu da mazan suke yi yana shafar rayuwarsu yadda suke dadewa ba tare da yin aure ba, amma hakan ba zai sa mata su daina karatun ba saboda abu ne da zamani ya zo da shi.

Sanyin gwiwar masu zurfin karatu

Ita kuma Zahra’u Isa ta bayyana rashin auren nasu da mazan ke yi a matsayin wani abu da ke sare gwiwarsu wajen ci gaba da karatu.

“Na san iyayen da a yanzu suna son ’ya’yansu su ci gaba da karatu amma saboda tsoron kada su zo su rasa mijin aure ya sanya suka ki sanya ’ya’yan nasu a makaranta.

“Suna jira sai sun samu miji ko kuma sai ma sun yi aure sannan su je su yi karatun a dakunan mazajensu,” inji ta.

Aure garkuwa ce ga mace, amma…

Daga Yola Jihar Adamawa, Aminiya ta tattauna da Balaraba Hussaini mai shekara 39 wadda ta yi karatun digirin digirgir kuma take aiki a manyan kamfanoni.

Balaraba ta ce ita ba ta ki yin aure ba domin aure kamar kariya ce ga mace, musamman idan tana aiki da sauran maza a kamfanin da take aiki, an fi fifita mata masu auren a kan su marasa auren.

Ta ce ba ta yi aure ba ne domin komai yana jiran lokacinsa ne, duk da yake ta ce ba ta sha’awar auren talaka wanda zai zo ya ci guminta na shekara da shekaru.

A cewarta “Maza ba su da amana.”

Shi ko Rabi’u Ibrahim ya ce ba ya sha’awar macen da ta tara shekaru da yawa.

Dalilinsa shi ne, “Namiji na son girmamawa, idan ka auri wadda idonta ya bude kuma ga dukiya a gaskiya biyayyar za ta yi wahalar samuwa, gara maka ’yar karama koda ko ’yar gidan talaka ce,” inji shi.

Cin duniya na tsinke

Ita ko Hajiya A’isha Mustapha mai shekara 41 ta ce tunda auren ba farilla ba ne kuma ita a rayuwarta ba ta son wani ya zo yana fada mata lokacin fita da lokacin dawowa, ta gwammaci ta yi ta cin duniyarta da tsinke.

Ta kara da cewa akwai halin da mace za ta nuna a zahiri wanda zai sanya a raina ta.

A cewarta mace idan ta kame kanta ba wanda ya isa ya zo ya tunkare ta da maganar banza ballantana raini.

Ruwa ba sa’an kwando ba

Aliyu Sama’ila ya bayyana cewa a ra’ayinsa zai iya auren macen da ta yi karatu mai zurfi.

Sai dai ya ce matsalar ita ce kamar yadda Hausawa ke cewa, hanyar jirgi daban ta mota ma daban ne ya sa bai son ko haduwa da su a hanya.

Da Aminiya ta tambaye shi game da yi musu magana ko ta shafukan zumunta, sai ya ce ai daga irin hotunan da ka dora ma ta san cewa kai ba ka da hali.

Ya ce shi da sauran samari da dama suna sha’awar auren su amma jan ajinsu ne ke hana su yi musu magana.

Mazan banza su yi yawa

Ita kuwa Fadila Nasiru ta ce akasarin mata ba kin auren ba ne suke yi, mazan banza ne suka yi yawa shi ya sa ta hakura tare da cewa idan ta samu wanda hankalinsa ya kai ya aure ta a shekararta 49, za ta aure shi amma ba ta son auren karamin yaro.

Ta kara da cewa rashin auren wadansu matan kuma na yiwuwa ne domin rashin son daukar nauyi.

“Maza da dama ba su daukar nauyin da Allah Ya dora musu musamman na ’ya’yansu.

“Za ki yi mamaki idan na fada miki cewa kashi 90 cikin 100 ba su sauke nauyin da Allah Ya dora musu na yara, bar wa matansu suke yi.

“Wannan dalilin ma ai dole ya hana ka sha’awar aure,” inji ta.

Kwarjinin mata ’yan boko

Muhammadu Hammangabdo ya ce tsoron irin wadannan mata yake yi domin maza da dama na sha’awar aurensu amma tsoron kada a watsa musu kasa a ido ke hana galibin maza taya su ko za a yi sa’a.

Ya ce ana samun wadannsu masu saukin kai kamar ba su yi zurfin karatu ba kuma kamar ba ’ya’yan gidajen masu dukiya ba, amma akasarinsu suna yi wa samari kwarjini ne.