✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da Sakkawata ke al’adar gasa dabbobi a lokacin sallah

Ko ba don Allah ba za ka yi don gudun kunyar idon mutane.

A kowace Sallah babba wadda aka fi sani da Sallar Layya, mutanen Jihar Sakkwato sukan yanke dabbobin ni’ima kamar sauran musulmai na duniya.

Sai dai su Sakkwatawa suna da wata al’ada ta gasa dabbobin layyarsu wadda ta haura shekara 200 suna yinta.

Sukan gudanar da wannan al’ada ta gasa dabbobin a lokaci daya a kungiyance wacce suke kira da TARENI.

Aminiya ta duba wannan al’adar ta hanyar jin ta bakin Sakkwatawan game da lamarin da suka gada kaka da kakanni.

Barista Bashir Mu’azu Jodi ya ce, “Wannan al’adar tafi shekara 100 ana  yinta haka muka taso muka ga ana yi.

Yadda Sakkwatawa ke gasa dabbobin layya

“Mun gode Allah muna jin dadin abinmu kuma kowace jiha ko yanki yana da al’adarsa, inda da an zo nan aka ga haka an jera raguna domin gasa su an san Sakkwato ce,” a cewarsa.

Naman da aka gasa  ya fi wanda aka soya dandano

Barista Jodi ya ce, yanayi ba guda ba domin su a wurin gashin suna sanya magi, inda a lokutan baya sukan sa gishiri amma sai suka fahimci bai inganta lafiya a jiki.

A cewarsa, idan naman da aka gasa da wanda aka soya ba su zama daya a wurin dandano, lamarin da ya ce na gashin ya fi.

Dalilin da muke al’adar gasa nama

“A yayin da nake yi wa al’ummar musulmi barka da Sallah, ba mu fatar wannan al’adar ta bace, ba mu ga alamar hakan ba, domin tun in da aka fito ba taba bari ba.

Yadda ake al’adar Tareni a Sakkwato

“Kuma muna yi ne domin rufe kofar rowa don ya kasance da mai hali da marar hali kowa zai ci nama a wadace a lokacin sallar layya,” a cewar Barista Jodi.

‘Bana ba kamar lokutan baya ba’

Ya ce “bana ba a cewa komai abubuwan sun yi nauyi idan aka dubi yanayin da ake ciki tattalin arziki ya samu matsala.

“A shekarar da ta gabata abin da ka saye dubu 50 ko 60, a bana za ka saye shi 100 da wani abu gaskiya ba a cewa komai sai godiya.”

‘Al’adar tana kara dankon zumunci’

Abdullahi Arzika Jaredi, ya ce al’ada ce da ke hada zumunci sannan ta kawar da bambancin akida da siyasa.

“A lokacin wannan gashi za ka samu dan Izala da ‘yan dariku duk a wuri guda haka za ka samu masu bambancin jam’iyya da yara da manya ma, inda dan shekara 60 zai zauna wuri daya da mai shekara 20.

Yadda aka jera raguna ana shirin gasawa a Sakkwato

Ya ci gaba da cewa “Bayan zumunci za ka samu ana taimaka wa juna wanda yake da karfi zai dauki wanda baya da shi, musamman a wurin gashin za ka samu mai kudi a unguwar zai sayi itacen da za a yi gashi shi kadai, ko wasu mutanen ‘yan kadan su saye amadadin saura.

“Za ka samu matasan kowace unguwa su ke tsayawa su yi aikin a sallame su don wani ba ya zuwa unguwar wasu ya yi aiki.

“Ba a samu hadin kai na duk al’umma a kowace unguwa a Sakkwato sai a wannan aikin na TARENI.

“Haka kuma ana rufe kofar rowa domin duk wanda ya yi layya a unguwar an san ya yi don haka zai taimaki wanda bai yi ba,” in ji Jaredi.

Tana rufe kofar rowa

Sadiya Attahiru ta ce, “babban abin da ya sanya ake yin wannan al’ada ba zai wuce rufe kofar rowa ba domin da kunya ka yanka dabba a gasa ma gaban jama’a ka kasa baiwa wanda bai yi a unguwarku ba.

Ta ce, “ko ba don Allah ba za ka yi don gudun kunyar idon mutane, amma in a cikin gida ne aka yanka ma rago ka soya abinka sai in ka dubi Allah ne za ka yi sadaka.

“A ganina dalilin haka magabatanmu suka fito da wannan al’adar domin a rika taimakon juna musamman wanda ya yanka rago ya bai wa wanda bai yi ba abin da ya sauwaka”a cewar Sadiya.