✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da na ziyarci Fulanin hanyar Kaduna zuwa Abuja —Dokta Gumi

A ranar Lahadin da ta gabata ce fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Dokta Ahmad Gumi ya ziyarci wadansu Fulani da ke dajin Jere a hanyar…

A ranar Lahadin da ta gabata ce fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Dokta Ahmad Gumi ya ziyarci wadansu Fulani da ke dajin Jere a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A zantawarsa da Aminiya Shaihin Malamin ya bayyana dalilansa na shiga dajin don ganawa da Fulanin duk da hadarin da ke tattare da yin haka:

Mene ne dalilin ziyartar daji da ka yi don ganawa da Fulani a hanyar Abuja zuwa Kaduna?

Kowa ya san batun tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Kuma sai muke jin cewa duk wanda ’yan sanda ke kamawa idan aka tambaye shi ko ya iya Fatiha sai ya ce bai iya ba, ko ya iya wani karatun boko sai ya ce bai yi ba.

Sai muka gane cewa wadannan mutane jahilcinsu ya sa ake amfani da su.

Muka gane ba wani kudi ake ba su ba ana amfani da su ne suna cutar da kansu suna cutar jama’a.

Sai muka ga maganin abin shi ne na daya a shiga cikinsu a nuna musu kauna sannan a nuna musu abin da ya kamata su sani na addini.

Da kuma abin da ya kamata su sani na rayuwarsu ta duniya. Abin da ya sa muka je ke nan.

Sheikh Gumi a lokacin da halarci wurin yi wa Fulani wa’azi a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Wace hanya ka bi wajen gayyatar Fulanin har suka amince suka halarci taron?

Idan ka san manyan Fulani kuma ka nemi su taru idan har suka amince maka kuma suka yarda da kai za su zo.

Tunda sun san ba an zo ne domin yin amfani da su a cimma wata manufa ta son kai ba.

Kuma sun san duk kungiyoyi da suke yin amfani da sunansu domin yin kudi da cutar su. Amma idan sun yarda da kai za su zo.

Da ka shiga me ka gani ko ka lura da shi?

Abin da na gani shi ne su kansu, kansu ba a hade yake ba.

Akwai masu kokarin hana ta’addanci a cikinsu amma suna tsoron masu ta’addancin da ke cikinsu.

Su kuma ba su iya yin wani abu domin babu mai taimaka musu idan an kai musu hari.

Ashe ke nan ka ga dole sai an hada al’ummar gaba daya, a koyar da ita kuma a yi tsarin da za a taimaka musu, domin su ji dadin gwamnati kamar yadda sauran mutane suke ji.

Wasu daga cikin masu sauraron wa’azin

Wadansu na ganin hadari ne shiga dajin da ka je. Ko Malam zai fada mana yadda ya ji kafin yin wannan tafiya?

A’a ai idan ba ka tari hadari daga nesa ba, zai zo ya same ka a gida.

Saboda haka ko da mun tsaya ba wai mun tsira ba ne; Gara mu fita mu tare shi a can.

Kuma alhamdulillahi mun same su suna da saurare kuma suna son a yi musu wani abu da zai sa su bar wannan abu.

Akwai wadansunsu da suka zo wurin kusan su hamsin da suka ce sun tuba sun bar wannan aiki. Shi ne muka ce a siturta su.

Yanzu muna son a yi kidayar sanin kowa domin a ba shi taimako da kuma kariya; saboda nan gaba idan an yi barna an san ba shi ba ne.

Ke nan daga cikin mutanen da suka halarci wurin akwai masu aikata laifin ke nan?

Eh, akwai su kusan sun fi hamsin da suka tuba.

Ko ka samu wata gudunmuwa daga gwamnati ko ku ne kuka dauki nauyin kanku?

Tunda gwamnati ta ba mu ’yan sanda ka ga ke nan akwai goyon bayan gwamnati, amma ba ita ce ta tura mu ba, mun je ne da kanmu.

Muna ganin cewa idan ana son zaman lafiya su kansu Fulani na bukatar a koya musu abin da ya kamata kuma a nuna musu su ma ’yan kasa ne, sannan a daina nuna musu wariya.

Baya ga waazin da ka yi musu kan batun neman ilimi me ka fada musu?

Abin da na fada musu shi ne wake daya ke bata gari saboda haka hana ta’addanci su ne za su iya, domin su suka san ’yan ta’addan cikinsu.

Saboda haka a yi kwamitin tsaro idan an samu dan ta’adda kwamiti za a gaya wa domin idan daidaiku suke kai kara wurin ’yan sanda sai a bi su a rika kashewa amma idan kwamiti ne za a samu sauki.

Domin suna samun matsala wurin ’yan sanda a kan yi wa mutum coge a ce ya yi abu alhalin bai yi ba; Wani lokaci sai sun sayar da shanu kafin su fanshi mutum.

To, ka ga idan an yi kwamitin tsaro a tsakaninsu insha Allah za mu samu saukin abin.

Muna kuma son gina musu makaranta da wurin da za su rika shayar da dabbobinsu.

Wasu daga cikin masu sauraro a lokacin da Sheikh Gumi yake wa’azin

Ko akwai wani kokari da za ka yi wurin shiga tsakani ta hanyar fahimtar da jami’an tsaro su kauce wa kama mara laifi suna rufewa?

Shi ya sa muke son kafa kwamitin tsaro wanda za mu saka lauyoyi da manyan jami’ai namu da suka yi ritaya na janar-janar, ya zama duk wanda aka kama sai mun bi mun tabbatar a kan ya yi laifin ne.

Domin a yanzu haka an ce akwai da yawa da aka kama ba masu laifi ba ne aka yi musu irin wannan karya, za mu ga an fitar da su daga kurkuku.

Ko akwai wani kira da za ka yi ga kungiyoyin addini su shigo domin taimakawa wurin wayar da kan Fulani kan addini?

Eh, ina kiran kungiyoyin addini su shiga mutanen nan, amma kada su je da sunan kungiyarsu.

Kowa ya ajiye kungiyarsu a garinsu, idan zai shiga daji ya shiga a Musulmi kawai.

Ya je ya koya musu yadda ake Sallah da yadda ake azumi da farillai domin mutumin da bai san shi mutum ba ne ta yaya za ka je masa da hayaniyar kungiya daga cikin gari?

Baya ga yankin Jere akwai wurare irin su Birnin Gwari da Giwa da Igabi da ke fama da rashin tsaro ko su ma za a kai musu irin wannan ziyara?

Duk inda suke idan har dan Adam zai iya tafiya wurin za mu shiga in Allah Ya yarda.

Mene ne kiranka ga gwamnati?

Kirana ga gwamnati shi ne su sani cewa ilimantar da al’umma irin wannan dole sai ta shigo ciki saboda haka gwamnati ta taimaka yadda za a gina musu makarantu a samar da malaman da za su koyar da su domin su ma su san ’yan kasa ne su.

Sannan a fahimtar da jami’an tsaro su daina wulakantar da Fulani a duk inda suka gan su.

Domin bai dace ba da an ga Bafulatani a cikin mota a saukar da shi a lika masa cewa ana tuhumarsa, wannan bai dace ba a nuna irin wannan wariya.