Tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Super Eagles, John Obi Mikel ya bayyana dalilin da ya sa ya daina buga wa kungiyar kwallo.
Mikel ya yi ritaya daga yi wa Eagles kwallo jim kadan bayan kammala Gasar Cin Kofin Afirka da aka yi a Masar inda Najeriya ta gama a matsayi na uku.
Mikel ya ce ganin yadda ya fara tsufa ne ya sa ya daina buga wa kungiyar wasa, inda ya bar wa matasa masu tasowa dama.
Ya kara da cewa, shekaru sun fara yi masa nisa don haka ya yanke shawarar mayar da hankali a kan yi wa kulob dinsa wasa maimakon Najeriya.
“Akwai yiwuwar in yi ritaya daga kwallon kafa nan gaba kadan don haka na daina yi wa Eagles kwallo,” inji shi.
Mikel ya fadi wadannan kalamai ne a karshen makon jiya a hirar da ya yi da wata mujallar da kulob dinsa na Trabzonspor da ke Turkiyya ke wallafawa.
Mikel ya yi wa kulob da dama wasa a Turai ciki har da na Chelsea da ke Ingila, kafin ya canja sheka zuwa kulob din Trabzonspor na Turkiyya a bara.