Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilan da ya amince aka sauya fasalin takardun kudi – N200, N500 da kuma 1000.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da sabbin takardun kudin a Abuja, Buhari, ya ce ya bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN), izinin sake fasalin kudin ne saboda Naira ta jima a haka shi ya sa ya bukaci a sauya mata fasali.
- Martani: Ba jiharmu ce ta fi ko’ina talauci ba a Najeriya – Sakkwato
- Dan bindiga ya harbe mutum 10 a kantin sayar da kaya a Amurka
A cewar Buhari, “An yi wa sabbin takardun kudin Naira karin tsaro ta yadda zai yi wahala a buga jabunsu.
Buhari ya kara da cewa, “A farkon wannan shekara ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gabatar min da bukatar sauya fasalin kudin kasar nan, kuma na yi nazari sosai kafin na amince, na kuma bayar da izinin aikata hakan.
“Akwai bukatar a dauki matakin gaggawa na kula da kudaden da ake yawo a kasuwannin kasar nan, da kuma dakile fadurwar darajar Naira a tsarin banki, da karancin takardun kudi masu tsafta da inganci da ake yawo da karuwar jabun takardun kudi a tsakanin al’umma.
“Saboda haka ne na bayar da izinin a sauya fasalin N200, N500 da kuma N1000,” in ji Buhari.
A safiyar ranar Laraba ce Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin kudin da aka sauya wa fasali a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.