✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da mutane suka fara ‘hukunta’ masu kwacen waya a Kano

Amma 'yan sanda da lauyoyi sun ce yin hakan ba daidai ba ne

  • Ba daidai ba ne—’Yan sanda

An dauki kimanin shekara biyu al’ummar Jihar Kano suna fuskantar matsalar kwace ko fashin waya inda batagari wadanda yawancinsu matasa ne masu kananan shekaru suke tare mutane suna kwace.

Rahotanni sun ce ba wai kwacen waya wadannan matasa ke yi ba, sukan yi amfani da makamai wajen raunata mutanen da suka kwace wa wayar kafin ko bayan sun kwace musu. A wasu lokutan ma sukan kashe mutanen.

Duk da cewa masu kwacen wayar sun fi gudanar da mummunan aikinsu a cikin dare, akan samu ire-iren wuraren da ake gudanar da kwacen wayar da rana, ido na ganin ido.

Wannan matsala ta zama ruwan dare domin zai yi wuya a samu iyalin da ba su taba dandanar wannan abin takaici na kwacen waya ba. Idan kai ba a yi maka ba to an yi wa wani naka.

Kuma masu kwacen wayar suna da salo-salo kan yadda suke gudanar da aikinsu inda wasu ake kwace musu waya a yayin da suke tafiya wasu kuma a kwace musu wayar a lokacin da suka hau keken nan mai kafa uku.

Aminiya ta ruwaito yadda mutane da dama suka sha da kyar a hannun masu kwace wayar, inda suka tsira da raunuka.

‘Yadda aka kwace mana waya’

Wata mai suna Zainab Yusuf ta ce tana kan hanyarta ta zuwa aiki sai ta ga wani keke mai kafa uku ya zo kamar zai wuce ta kusa da ita.

“Ban yi aune ba, sai na ji an fisge jakata. Sai na kai hannu zan karbe jakar sai daya daga ciki ya sa wuka ya sare ni a hannu. Nan na fadi cikin jini kafin daga bisani jama’a su kawo kin dauki inda aka kai ni asibiti,” in ji ta.

Wani da ya taba shiga hannun ’yan kwacen wayar ya ce, “Ina cikin keke mai kafa uku, to na samu wasu a ciki. Ban sani ba ashe tare suke da direban. Muna cikin tafiya sai direban ya rika yin wani irin tuki. Sai ya zama muna yin sama da kasa.

“Ya zama ni da wanda ke kusa da ni muna haduwa da juna. Ashe ban sani ba a wannan lokaci wanda ke zaune kusa da ni ya sa hannu a aljihuna ya dauke min waya. Sai da na sauka ina kokarin dauko kudi in ba wa direban sai kawai na ga ya ja keken cikin sauri. A lokacin na gane cewa sun dauke min waya.”

A baya-bayan nan Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya ce ’yan sanda za su rika gurfanar da wadanda aka kama da laifin kwacen waya a matsayin ’yan fashi da makami.

Kuma a ranar Talatar da ya fadi haka ne aka samu wasu matasa sun kone wani babur din masu kwacen wayar bayan da suka tsare wasu mutane suka karbe musu waya.

Wata ganau ta shaida wa Aminiya cewa, “Masu kwacen wayar sun taho ne daga titin Rijiyar Zaki, bayan da wani daga cikin mutanen da suka kwace wa waya ya yi ihu ne mutane suka yi kokarin kama su inda suka cika wa wandonsu da iska suka tsallake suka bar babur din.”

Kwamishinan ya yi haka ne domin samun sauki lamarin ta hanyar firgita matasan, domin zaman gidan yari mai tsawo ne laifin fashi da makami.

Me ya sa aka fara daukar doka a hannu?

Sai dai duk da wannan furuci na Kwamishinan ’Yan sandan da kamen da ’yan sanda suka rika yi, matsalar tana ci gaba da ci wa mutane tuwo a kwarya, wanda hakan yake fusata mutanen gari.
A kwanakin baya an rika sanya hotunan wadanda masu kwacen waya suka kashe, inda Aminiya ta ga hotunan sama da 20 da ake yadawa a Facebook, sai dai Aminiya ba ta tantance sahihancin hotunan da lokacin da aka kashe su ba.

Sai dai wadannan hotuna sun kara tunzura mutane, inda suka fara cewa ya kamata a fara daukar doka a hannu ana hukunta su.

A karshen makon jiya wasu matasa a Unguwar kofar Kabuga suka kone wani babur mai kafa uku a kokarinsu na daukar fansa a kan wasu matasa da suka yi kokarin kwacen waya a hannun wani matashi bayan matasan da ake zargin sun tsere.

Daya daga cikin matasan kofar Kabuga ya shaida wa Aminiya cewa, “Wadannan matasa sun yi kokarin kwace wayar wani matashi a nan unguwar, Allah Ya sa ya yi ihu, hakan ya ja hankalinmu muka zo wurin don kai masa dauki, sai dai kafin mu zo sun riga sun gudu sun bar babur dinsu a wurin. Hakan ya sa muka kone babur din.”

A cewar matashin da sun samu masu kwacen wayar, “Wallahi da sai mun kone su kurmus. Kuma wallahi ko gobe wasu suka sake shigowa unguwarmu za su kwace mana waya, to wallahi sai mun kone su kamar gawayi,” in ji shi.

Da yake bayyana dalilinsu na daukar wannan mataki ya ce, “Lura da cewa hukuma ba ta daukar mataki a kan masu kwacen wayar ya sa muka ga cewa mu da kanmu za mu rika hukunta su.”

A ranar Litinin da ta gabata ma an samu irin hakan a Kuka Bulukiya a Karamar Hukumar Dala inda wasu matasa suka yi wa wasu masu kwacen waya dukan kawo wuka.

Haka a ranar Talatar da ta gabata an samu rahoton cewa matasa suka kone babur mai kafa uku a daidai Shatalelen Asibitin Nasarawa daidai lokacin da aka biyo su bayan sun yi fashin waya a kan Titin kofar Kudu, Gidan Sarki.

A karshe an yi nasarar kama matasan inda aka yi musu dukan kawo wuka har ana zargin daya daga cikinsurai ya yi halinsa. Rahotanni sun ce tuni aka iza keyar sauran zuwa ofishin ’yan sandan Kano.

Daukar doka a hannu ba daidai ba ne  ’Yan sanda

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce duk da cewa masu kwacen wayar laifi suke aikatawa, amma daukar doka da mutane ke yi da kansu ba daidai ba ne.”

“Idan mun duba masu kwacen waya laifi suka aikata, amma abin da mutane suka fara yi na daukar doka a hannu ba daidai ba ne, kuma mu a Rundunar ’Yan sanda ba ma maraba da wannan lamari.

“Idan muka kama duk wanda ya dauki doka a hannu za mu yi masa hukunci daidai da laifin da ya aikata,” in ji shi.

SP Kiyawa ya musanta zargin da jama’a ke yi cewa ba sa hukunta masu kwacen waya, inda ya ce, “Ba gaskiya ba ce mutane su fito su ce ba mu hukunta masu kwacen waya domin al’umma shaida ne kusan kullum muna kama wadannan mutane kuma muna kai su kotu. Kowa ya san yadda ake gudanar da shari’a ba wai kawai daga zuwa ake yanke musu hukunci ba, dole sai alkali ya bi komai daki-daki kafin ya kai ga yanke hukunci. Abin farin ciki shi ne a yanzu Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya fitar da doka cewa duk wanda aka kama da kwacen waya to za a yi masa shari’ar masu fashi da makami ne.”

A wani taron manema labarai Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Muhammad Usaini Gumel ya yi nuna wasu matasa kimanin 65 wadanda ake zargi da laifin kwacen waya a jihar. Haka kuma Kwamishina Gumel ya yi baje-koliin wasu makamai kimanin 150 da ya ce an same su ne a hannun matasa masu kwacen wayar.

Daukar doka a hannu ba zai haifar da da mai ido ba-Barista Abba Hikima

A bayanin Barista Abba Hikima Fagge, lauya mai fafutikar kare hakkin dan Adam a Jihar Kano ya ce daukar doka a hannu da mutane ke yi ba abu ne mai kyau ba, kuma ba zai haifar wa al’umma da mai ido ba.

“Duk da cewa masu kwacen waya laifi suka aikata amma hakan ba zai zama hujja ga al’umma su rama abin da ake yi musu ta hanyar daukar doka a hannunsu ba, domin hakan ya saba wa doka. Ba zai yiwu a warware laifi da aikata wani laifin ba,” in ji shi.

Malam Usman Abba, malamin addinin Musulunci a Jihar Kano ya ce addini ya yi hani ga mutane su dauki doka a hannunsu.

“A gaskiya addinin Musulunci ya yi hani a kan daukar doka a hannu. Duk wanda ya yi maka wani abu na laifi kamata ya yi ka kai kararsa gaban hukuma don a bi maka hakkinka. Idan kuma ka dauki doka a hannunka to babu shakka ka aikata abu na laifi,” in ji shi.

Wata kungiya mai yaki da shaye-shaye a Jihar Kano ta gudanar da taron wayar da kai a kan yadda gwamnati da al’umma za su magance matsalar kwacen waya a tsakanin al’umma.

Shugabar kungiyar Zainab Nasir Ahmad ta ce, “Dole ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan al’amuran tsaro a fadin jihar. Haka kuma su ma jama’a su daina fito da waya fili a lokacin da suke tafiya a bainar jama’a.”