✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da muke bambanta masu kudi da talakawa a aikinmu – Hisbah

Hisbah ta kuma musanta cewa ba ta hukunta masu hannu da shuni.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana dalilan da ya sa ake ganin tana bambanta talakawa da masu kudi a aikinta duk lokacin da za ta hukunta masu saba wa shari’ar Musulunci.

Hukumar ta kuma musanta cewa ba ta hukunta masu hannu da shuni a duk lokacin da suka aikata wani laifi makamancin na talakawa, inda ta ce kawai dai hanya daba-daban take bi wajen yin hakan.

A ’yan kwanakin nan ne dai hukumar ta sha suka kan yadda ta rufe idanunta kan irin shigar da ’yar Sarkin Bichi, Zahra Bayero ta yi yayin shagalin bikinta da dan Shugaban Kasa, Yusuf Buhari.

Sai dai a yayin wata tattaunawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano, wani Darakta a hukumar, Aliyu Kibiya ya ce sukar shugaba a bainar jama’a ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

“Ko da yake muna wa’azi ga dukkan sashe na al’umma kan su yi abin da ya dace, amma mukan yi hakan ne a mataki-mataki.

“Ba ya cikin koyarwar addinin Musulunci, alal misali, mutum ya hau mumbari yana sukar shugabanni. Akwai hanyoyin jawo hankalinsu ba tare da an yi kwarmato ba,” inji Aliyu Kibiya.

A wani labarin kuma, Babban Kwamandan hukumar, Harun Muhammad Ibn Sina ya shaida wa gidan rediyon na Freedom a wata hirar ta daban cewa hukumar ta kama ’ya’yan masu kudi da dama a lokuta daban-daban, kuma tana ci gaba da yin hakan.

Ko da yake Kwamandan bai ambaci sunan ’ya’yan wadanda hukumar ta kama ba, ya ce ba hukumar ba ta daga kafa ko kadan ga duk wanda ya aikata badalar da ta saba wa shari’a.