✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da muka tsawaita yajin aikinmu da sati 8 – ASUU

Kungiyar ta ce ta tsawaita wa’adin ne don ta ba gwamnati damar cika alkawuran

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta sanar da tsawaita yajin aikin mako hudun da ta fara yi saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawuran da suka kulla a shekarar 2020.

Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

A cewarsa, Majalisar Zartarwar Kungiyar ta Kasa a yayin taronta na ranar Lahadi, ya ce sun yanke shawarar tsawaita yajin aikin da mako takwas don ba gwamnatin damar aiwatar da yarjejeniyar.

Sanarwar ta ce, “Majalisarmu tana godiya da kokarin shiga tsakani ta hanyoyin dalibai da iyaye da ’yan jarida da kungiyoyin fararen hula da sauransu, wajen magance matsalar.

“Sai dai ASUU a matsayinta na kungiyar mutanen da suka san ya-kamata, tana da hakkokin da gwamnati ya kamata ta girmama.

“A sakamakon haka, mun yanke shawarar tsawaita yajin aikin da mako takwas don ta ba gwamnati dama, ko dalibai sa samu damar komawa makarantu.

“Tsawaitawar za ta fara aiki ne daga karfe 12:01 na safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Maris na 2022.”