✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da muka hada bikin shan rake’

Sun shirya bikin yadda kowa zai sha iya iyawarsa don samun zaman lafiya

Matasan unguwar Dorayi a Jihar Kano sun bullo da sabon bikin shan rake a tsakaninsu wanda suka gudanar a karshen makon jiya.

Bikin wanda shi ne karo na biyu, ya gudana ne a ranar bikin auren wadansu daga cikin jagororin bikin.

A lokacin bikin, matasan sun yi shiga ta barkwanci don kara wa bikin armashi inda wadansu daga cikinsu suka yi ado da gashin kaza a matsayin gemu da sauransu.

Abba Is’hak Dansoja shi ne shugaban shirya taron, ya bayyana cewa suna shirya bikin ne don samun hadin kai a tsakanin matasan yankin tare da nishadantar da jama’a.

“Daga yadda kuke gani kowa yana cikin farin ciki da walwala, wanann ya isa ya nuna muku yadda muke zaune lafiya da juna wanda kuma muke son dorewar hakan a tsakaninmu.

“Ba wani abu muke gudanarwa ba, illa muna zama mu sha rake iyakar iyarwarmu tare da yin raha a tsakaninmu,” inji shi.

A cewarsa, duk da cewa a bana rake ya yi tsada, amma hakan suka daure suka samar da isasshen rake wanda kowa zai sha iyakar iyawarsa.

Ya ce bikin na bana ya fi na bara tara jama’a don haka tun yanzu suna tunanin fara shirin na badi don ganin ya gamsar da jama’a.

“Bikin na bana ba kamar na bara ba wanda muka yi shi a tsakaninmu matasan yankin kadai.

“A wannan lokaci mutane da dama daga wurare daban-daban sun halarta, kuma muna ganin hakan ya faru ne saboda tallata bikin na bana da muka yi a kafafen sada zumunta na zamani .

“A yanzu haka za mu daura damarar yadda za mu shirya bikin badi don ganin ya kayatar da jama’a,” inji shi.

Abin da ya sa na shiga cikin maza wajen bikin –Zainab

Wata kallabi tsakanin rawuna da ta shiga jerin matasan mai suna Zainab Umar, ta shaida wa Aminiya cewa ta ji dadin halartar bikin domin a cewarta bikin yana sauke wa mutum duk wata damuwa.

“Na tabbata duk wanda ya zo wurin nan yana cikin nishadi, domin ko hawan jini kake da shi to zai sauka cikin kankanen lokaci.

“A yanzu haka na kusa kammala shan sanda biyu na raken. Ni kaina mamakin kaina nake,” inji ta.

Wani da ya halarci taron ya bayyana cewa, “Ba zan taba yarda in ki halartar bikin ba saboda tun farko dama ni mutum ne mai son rake sosai.

“Kun san rake akwai zaki sannan akwai dauke hankalin mutum daga abin da yake yi saboda santi,” inji shi.

Mun karfafa wa matasa gwiwa ne saboda zaman lafiya –Mai  unguwa

Daga cikin mahalarta bikin akwai Mai unguwar Dorayi bangaren Unguwar Bello Alhaji, wanda ya shaida wa Aminiya cewa ya zo taron ne don ya karfafa wa matasan yankin gwiwa tare da ba su goyon baya kan abin da suke yi.

“Lura da cewa wannan biki da suka shirya bai saba wa addini ko alada ba.

“A tunaninmu ma abu ne da zai kara musu hadin kai a tsakaninsu don haka muka ba su goyon baya.

“Da a ce matasan sun je suna shan muggan kwayoyi ai gara a ce rake suke sha,” inji shi.