Miliyoyin Musulmi ne suka halarci taron Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani da Khalifansa Shehu Ibrahim Nyass a garin Bauchi, bayan da cutar Kwarona ta sanya aka yi hakan.
Taron wanda aka yi a karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu halartar wakilan gwanonin jihohin Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Khalifan Tijjaniyya a Masar, Sheikh Muhammad Ahmad Al-Hafiz da Khalifan Shehu Ibrahim, Sheikh Mahiy Nyass wanda Sheikh Baba Lamin ya wakilta da sauran manyan malamai daga kasashen Senegal da Mauritaniya da Mali da Nijar da wasu kasashen Larabawa.
- Abinda ya sa muka daga maulidin bana – Sheik Dahiru Bauchi
- Maulidi na nuna karfin Musulunci ne- Sheik Dahiru Bauchi
An gabatar lakcocin “Makon Shehu” a otel din Zaranda, inda aka yi karatuttuka kan rayuwar Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Nyass da gwagwarmaryarsu da bayanin Darikar Tijjaniyya Cikin malaman da suka gabatar da maqala akwai Farfesa Ibrahim Makari da Khadi Mustafa Umar Suleiman da Sayyid Mustafa Adinga da Dokta Lawi Shehu Atik da Dokta Bashiru Sheikh Dahiru da Dokta Fatihi da Malam Naziru Dahiru Bauchi da sauransu.
Jagoran taron, Shehu Dahiru Usman Bauchi ya shiga wajen taron daga baya, inda ya fito ta saman motarsa yana zagayawa cikin jama’a yana yi musu addu’a, inda yawan jama’a ya sa Shehin bai samu shiga wajen da aka shirya zai zauna ba sai dai a kan motar da yake zaune ya yi jawabi.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce Maulidin Shehu Ibrahim da ake yi kowace shekara cikin watan Rajab bara ba a samu yi ba saboda bullowar cutar Kwarona, shi ya sa da lokacin yin Maulidin Shehu Tijjani ya zo cikin watan Safar sai aka gwama maulidan biyu aka yi su lokaci guda.
Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi addu’o’i masu yawa don samun zama lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya ya ce an shirya taron ne domin a nuna karfin Musulunci, a kuma nuna haskensa a kuma girmama bayin Allah Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim
(RTA).
Ya ce “Ina ba al’ummar Musulmi shawara mu hada kanmu, mu so junanmu, mu taimaki junanmu. Kada mu taimaki masu neman watsa jama’a, duk mai neman kafirta Musulmi yana neman watsa jama’ar Musulmi ne. Ya nuna wa duniya cewa shi ba ya son jama’ar Annabi
Muhammadu su yi yawa, ya fi son jama’ar Shaidan su yi yawa. Wanda ya zama Musulmi ai ya zama daga cikin jama’ar Annabi, idan ka ce ya zama kafiri ko mushriki ka kwashe wadannan mutane daga gidan Annabi ka mayar gidan Shaidan. Don haka nake kira mu rike hadin kai, mu kaunaci juna.”
A jawabin, Sheikh Baba Lamin Nyass ya nanata muhimmancin ’yan uwantaka da kaunar juna a tsakanin al’ummar Musulmi.
Ya yi addu’a domin samun zama lafiya tare da roqon Allah Ya yaye cutar Kwarona.
Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulqadir wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabi’u Baba ya wakilta ya gode wa malamai saboda addu’o’in da suke yi domin samun zaman lafiya.
Sai ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da malamai da shugabanni domin samun zama lafiya.
Shugaban Kwamitin Shirya Maulidin, Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, ya gode wa malaman da suka zo daga kasashen duniya, sannan ya shawarci mahalarta su ci gaba da bin dokokin kula da lafiya domin samun nasarar kawar da cutar Kwarona aduniya.
A lokacin taron an karrama tsohon Gwamnan Jihar Imo
Sanata Rochas Okorocha, saboda yadda yake goyon bayan
almajiranci da almajirai a Nijeriya da kuma yadda ya bude makarantu a jihohi da dama a Arewa.
Da yake yin godiya, Sanata Okorocha ya shaida wa taron cewa almajiri ba abin kaskantarwa ba ne kuma karatun Alkur’ani ba bara ba ne, neman ilimi ne, inda ya ce ko a boko ana tafiya daga wani gari zuwa wani gari don nemi ilimin boko.
Sai ya roki ’yan Nijeriya musamman masu hali su taimaka a kyautata rayuwar almajirai domin ci gaban ilimi a kasar nan.