Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta bayyana cewa ta gayyaci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Mista Femi Fani-Kayode, a ranar Litinin don gudanar da bincike kan wasu kalamai da ya yi.
Kakakin DSS, Dokta Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
- Muna goyon bayan takarar Tinubu —Shugabannin Fulani
- Za mu hukunta duk wanda ya ki karbar tsoffin kudi —Ganduje
Afunanya, ya ce binciken ya shafi wasu zarge-zarge na batancin da tsohon ministan ya yi kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa.
Ya ce hukumar ta gayyaci Fani-Kayode inda ya amsa tambayoyi kafin daga bisani ta ba da belinsa.
Ya ce an umarci tsohon ministan da ya rika zuwa ofishin DSS daga ranar Laraba har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansa.
Afunanya ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da kafofin yada labarai da su yi taka-tsan-tsan da kalamansu yayin da Babban Zabe ya karato.
Ya kara da cewar ‘yan siyasa su guji haifar da tarzoma ko kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar nan.
A ranar Litinin ne DSS ta gayyaci Fani-Kayode kan kalamansa na cewar dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan dakarun soji sun hada baki a kokarin kitsa murde zaben 2023 da ake shirin shiga.