✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa

A ranar Alhamis Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan har na tsawon watanni shida.

Majalisar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar.

A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar.

“An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne laifinta babu daɗi babu ragi.”

Sanarwar ta ce da a ce Sanata Natasha ta yi aiki da dokoki da ƙa’idojin majalisar, da majalisar za ta karɓi ƙorafinta, kamar yadda doka ta tanada.

“Amma ba ta bi ƙa’ida da dokokin da suka kafa majalisar da take aiki a cikinta ba.”

Sanata Bamidele ya ce majalisar ta ɗauki matakin dakatar da Sanata Natasha ne bisa shawarar kwamitin ɗa’a, wanda ya same ta da laifin saɓa wa sashe na 6.1 da sashe na 6.2 na dokokin majalisar.

Sanarwar ta kuma zayyano wasu laifuka biyar da ta ce Sanata Natasha ta aikata, ciki har da ƙin zama a kujerar da aka sauya mata a lokacin zaman majalisar na ranar 25 ga watan Fabrairu, da yin magana ba tare da amincewar jagoran zaman majalisar ba, da yin kalaman zagi da rashin girmamawa da shugabancin majalisar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan har na tsawon watanni shida a kan laifin saɓa wa dokokin majalisar.