Hukumar Hana Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta bayyana dalilin da ya sa ta cafke tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, awanni kadan bayan ya mika mulki ga Farfesa Charles Soludo.
Obiano, wanda ya mika mulki ga Soludo a ranar Alhamis, ya shiga hannun EFCC ne da misalin karfe 8:33 na daren ranar a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Legas, yayin da ya ke kokarin ficewa da Najeriya zuwa Amurka.
Ya zuwa yanzu dai EFCC ba ta bayyana laifin da ya sa ta cafke tsohon gwamnan na Anambra ba.
Sai dai kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya shaida wa manema labarai cewa tsohon gwamnan na cikin mutanen da hukumar take halin su, amma kariyar da yake da ita a matsayinsa na gwamna ya hana hukumar kama shi.
“Obiano ya jima a cikin komarmu tun ba yanzu ba. Amma yana da kariya a matsayinsa na gwamna shi ne dalilin da ya sa ba mu cafke shi ba tun tuni.
“Amma yau ya rasa wannan kariyar shi yasa muka cafke shi tun kafin ya fice daga kasar.”