✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da LP za ta zama babbar jam’iyyar adawa a bana — Peter Obi 

Za mu tsaya tsayin-daka a kan ayyukanmu na hadin gwiwa wajen gina kasa.

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya ce jam’iyyar LP (Labour Party) za ta zamo babbar jam’iyyar adawa a Najeriya a bana.

Obi wanda ya yi takarar Shugaban Kasa a zaben 2023, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a cikin sakonsa na taya ’yan Najeriya murnar shigowar sabuwar shekara ta 2024.

Tsohon Gwamnan ya bayyana cewa za a samu kyakkyawan ci gaba a Najeriya duk da cewa akwai muradun ’yan kasar da kawo yanzu ba su tabbata ba.

A cewarsa, “Nijeriya ita ce kasa daya tilo da muke da ita mai matukar baiwa, amma ta rasa samun shugabanci nagari tsawon shekaru.”

Ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta ci gaba da jajircewa don ganin ta daidaita a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya.

Obi ya ce dole ne al’ummar kasar su tashi tsaye wurjanjan domin kaucewa tafarkin jagoranci a karkashin jam’iyya daya kacal.

Haka kuma, ya ce akwai bukatar a tashi a farga domin dakile katsalandan din da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen shiga cikin harkokin cikin gida na jihohi, musamman a yanayin da ke barazana ga tsaron kasa.

Ya kara da cewa: “Mu a jam’iyyar Labour, mun dauki matakin ne don maslahar kasa da kuma sadaukar da kai wajen ganin Najeria sabuwa, kuma za mu tsaya tsayin daka a bangaren adawa, don haka, dole ne mu mai da hankali kan ci gaba.

“Za mu tsaya tsayin-daka a kan ayyukanmu na hadin gwiwa wajen gina kasa da ya zama wajibi da kuma la’akari da muhimmancinsa,” in ji Obi.

Ya ce: “Ina so in gode wa mambobin jam’iyyar Labour Party da dukkan magoya bayanmu da ake yi wa lakabi da Obidient, da masu yi wa Najeriya fatan alheri saboda amincinsu, juriya da jajircewarsu a kan dimokuradiyya ta hakika.

“Za mu ci gaba da tattaunawa da kokarin ganin jam’iyyar Labour ta zama babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya.

“Za mu ci gaba da hada kan dukkan ‘yan Najeriya da abokanmu, wadanda a yanzu suka fahimci babban tasirin hanyar da ba a dauka ba.

Da yake mika sakon gaisuwarsa ga daukacin ‘yan Najeriya, Obi ya yi addu’ar Allah Ya saka musu da alheri Ya kuma biya musu bukatunsu na alheri a cikin sabuwar shekara da ma shekarun da za su zo nan gaba.

Obi ya ce: “Abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata yanzu sun kasance cikin tarihin kasarmu. Sannan za mu ci gaba da lura da halin da al’ummarmu ke ciki, kuma ba za mu tsahirta ba har sai fatan da muke da shi ya tabbata.

“Har yanzu mun kasa samun zaman lafiya da tsaro a yayin da ake ci gaba da samun karuwar zubar da jini da ke damunmu har a wasu lokutan ma su kasance fiye da yanayin yaki.

“Yanayin yadda aka kashe daruruwan ’yan Najeriya da mugun nufi a watan Disamba shi kadai kawai ya isa ya zame mana abin bakin ciki wanda kuma babu inda zai faru a amince da shi.

“Yayin da muke addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu, muna bukatar Gwamnatin Tarayya ta yi duk abin da ya kamata domin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma dakatar da sake aukuwar makamancin lamarin a kowane bangare na Najeriya.”

Ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar na bukatar sauyi duba da yadda rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki, fatara, rashin daidaito da sauran muhimman abubuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa ke karuwa.

NAN