Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa a Jihar Kano, ana rufe gidajen kaji da dama a mafi yawan yankunan jihar duk da tsadar kwai da kaji a baya-bayan nan.
An kuma tattaro rahotannin abubuwa dabandaban da aka danganta su da rufe kasuwancin kajin.
- Dalilin da ma’aikata suka tsunduma yajin aiki a Neja
- Zan tsaya takarar shugaban kasa idan Buhari ya umarce ni —El-Rufai
An bayyana cewa, abubuwan da suka haddasa durkushewar gidajen sun hada da: Tsadar abincin kiwo kajin da tsadar sababbin kyankyasa da fargabar kamuwa da cutar murar tsuntsaye da rashin kasuwa ga masu kiwon da dai sauransu.
Wadannan su ne manyan batutuwan da manoman ke fama da su don tsira a cikin sana’ar.
A cewar Alhaji Kabiru Husseini, wanda ya yi ikirarin cewa ya shafe sama da shekara 15 yana sana’ar kiwon kaji a Jihar Kano, ya zama abin ban sha’awa ba ma ga masu son shiga cikinta sana’ar ba, har ma da wadanda suka zuba jarinsu a sana’ar.
Ya bayyana cewa, buhun abincin kaji masu yin kwai da ake sayar da shi a farko a kan Naira dubu 3, yanzu ya zama Naira dubu 6 ko 7, yayin da dan tsakon da ake sayarwa tsakanin Naira 100 zuwa N150 yanzu ya zama Naira 400.
“Kowace shekara mai kiwon kaji a Jihar Kano yana komawa baya a sana’ar maimakon gaba, ciyarwar tana da tsada haka ma kajin.
A bayyane yake cewa, galibin wuraren kiwon kaji a jihar an karkasa su zuwa kananan jari kuma a bayyane yake cewa, ba kowa ba ne ke iya ci gaba da yin sana’ar a irin wannan mawuyacin hali.
Ina igaya muku cewa, sama da gonakin kaji 20 aka rufe a Kananan Hukumomin Kumbotso da Madobi kadai,” inji Kabiru.
Wani mai gidan kaji mai suna Shehu Bala ya ce, ya rufe gidan kajinsa kwanakin baya, bayan kamuwar su da cutar murar tsuntsaye da ta barke a jihar.
A cewarsa, ya rage yawan tsuntsaye a gonarsa, saboda tsadar kiwon da ake yi, kuma abin takaici kajinsa sun kamu da cutar murar tsuntsaye.
“Na gaji a gaskiya kuma a halin yanzu ina yin wasu harkokin kasuwanci maimakon kiwon kaji.
“Tsawon shekara 4 na rage yawan kajin gonata, saboda tsadar kiwon, na rage yawan ma’aikatana, kuma yanzu maganar murar tsuntsaye ta kara ta’azzara”, a cewar Shehu.
An binciko cewa, gonakin kaji a garin Gunduwawa da wasu sassan Kananan Hukumomin Warawa ma sun rufe kamar yadda ya faru a wasu wuraren kiwon kaji kwanan nan.
Akalla gidajen kiwon kaji takwas cutar mura ta Avian Flu da aka fi sani da murar tsuntsaye ta shafa kuma an kashe dubban kaji kamar yadda Ma’aikatar Noma ta jihar ce ta tabbatar da lamarin.
Da yake tabbatar da bullar cutar, Daraktan Dabbobi na Ma’aikatar, Dokta Bello Bala, ya bayyana cewa bayan tattara samfurin daga gidajen kiwon kajin da abin ya shafa, an tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye.
Bello ya kara da cewa, Gwamnatin Jihar Kano tare da hadin gwiwar Kungiyar Manoman Kaji ta Najeriya (PAN) tun daga lokacin suka dauki matakin dakile yaduwar cutar murar zuwa wasu gonaki.
Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu gonaki 8 ne suka kamu da cutar, sannan kuma an rage yawan dubban kajin domin gudun yaduwar cutar murar zuwa wasu gidajen.
Hakazalika, Shugaban Kungiyar PAN reshen jihar, Alhaji Umar Usman Kibiya, ya bayyana cewa, a lokacin da manoman jihar suka lura cewa kajin nasu na mutuwa gaba daya, sai suka gaggauta sanar da Kungiyar PAN reshen jihar, kuma nan take kungiyar ta dauki mataki.