Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce har yanzu yana ci gaba da jinyar tiyatar da aka yi masa a kafarsa a birnin Landan.
Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Majalisar Wakilai da suka fito daga Arewacin Najeriya a birnin na Landan.
- Babu kasar da ta ci gaba ta amfani da harshen aro – Masani
- Yadda tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Malawi ya harbe kansa a majalisa
Sun kai masa ziyarar ne karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase a ranar bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yancin kai [Juma’a].
Tinubu, wanda ya shafe kimanin wata uku a kasar ta Burtaniya, ya shaida musu cewa yana dada murmurewa.
Ya ce, “Cikin ikon Allah da kuma taimakon mutane irinku, ina dada samun sauki. Kawai dai tiyatar da aka yi min ce dole sai ta dauki lokaci,” inji Tinubu.
Fitattun ’yan Najeriya da dama ne dai ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka ziyarci Tinubun a inda yake jinyar a Landan.
Aminiya ta rawaito cewa ko a makon da ya gabata, an ga fastocin takarar Tinubu, wanda daya ne daga cikin masu sha’awar neman shugabancin Najeriya a 2023, a wasu tashoshin jiragen kasa na Landan.