✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da babu ranar dawo da jigilar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna —Ministan Sufuri 

Za a samar da na’urar tsaro ta musamman da za ta rinka sanya ido kan titin jirgin.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa babu ranar dawo da sufurin jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ya ce babu ranar da dawo da jigilar har sai an sako dukkanin fasinjojin da aka sace tare da samar da karin matakan tsaro.

Ministan ya bayyana hakan ne bayan da ya kai ziyarar duba tashar jirgin kasa da ke Idu a Abuja a Talatar nan.

Wakilinmu ya ruwaito Ministan yana cewa, za a samar da na’urar tsaro ta musamman da za ta rinka sanya ido kan titin jirgin.

A baya dai Majalisar Zartarwa ta Najeriya, ta yi watsi da bukatar da tsohon Ministan Sufuri, Rotomi Amaechi ya gabatar ta samar da kudin sayen wannan na’ura a kan Naira biliyan uku.

Ministan ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci a tabbatar da an ceto ’yan kasar da aka sace don sun koma ga iyalansu.

Injiniya Jaji ya ce muddin ba haka ba, za a ga kamar gwamnati ba ta damu ba, alhalin kuma gwamnatin na yin duk abin da za ta iya yi domin ta ga an sako su sun sake haduwa da iyalansu.

A ranar 28 ga watan Maris ne dai ’yan bindiga suka kai wa jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare, inda suka kashe wasu fasinjojin suka yi awon-gaba da wasu.

Tun daga wannan lokacin ’yan taddar suna sako mutanen da kadan-kadan, bayan da suka nemi gwamnati ta biya musu bukatunsu kafin su sake su.