✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC

Babu ayyukan a zo a gani idan ka duba biliyoyin kudin da ke shiga jihar.

Ƙungiya mai rajin kishin APC a Kano mai suna APC Patriotic Volunteers, ta ce shekaru biyun da jam’iyyar NNPP ta shafe tana mulkin jihar nakasu ne da ke nuna tsantsar rashin ƙwarewarta a gwamnatance.

A taron da ta gudanar da manema labarai a Kano, ƙungiyar bisa jagorancin shugabanta Alhaji Usman Alhaji (Wazirin Gaya) ta ce nazarin da ta yi wa salon mulkin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar mata da gazawarsa wajen haɓaka ɓangarori masu muhimmanci duk da makudan kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata, da kuma kudaden shiga na cikin gida da take samu.

“Babu ayyukan a zo a gani idan ka duba biliyoyin da ke shiga jihar.”

Kazalika kungiyar ta zargi gwamnan da wawure Naira biliyan 1.6 da aka ware domin sayen mai da sauran kayan aiki na tsawon watanni uku a ma’aikatar ruwa ta Kano, baya ga gazawa wajen biyan ma’aikata sabon mafi ƙarancin albashi.