✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba zan taba mantawa da Ali Nuhu ba – Auwal West

Muhammad Auwal Isah wanda aka fi sani da lakabin Auwal West fitaccen jarumin fina-finan Hausa ne. A zantawarsa da Wakilin Aminiya kwanakin baya, ya yi…

Muhammad Auwal Isah wanda aka fi sani da lakabin Auwal West fitaccen jarumin fina-finan Hausa ne. A zantawarsa da Wakilin Aminiya kwanakin baya, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya fara harkar fim da nasarorin ya samu da kuma kalubalen da ya fuskanta a harkar. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu fara da tarihinka a takaice…
Assalamu alaikum, sunana Muhammad Auwal Isah (West). An haife ni a garin Jos da ke Jihar Filato a shekarar 1979. Na yi makarantar firamare da sakandare duka a garin Jos. Daga nan ban ci gaba ba sakamakon rasuwar mahaifina, wanda dalili hakan na dawo Jihar Kano wajen kakannina a shekarar 1997, kodayake daga bisani na shiga harkar fina-finan Hausa a shekara ta 2000. Na fara ne da wani fim mai suna ‘kudiri’, amma a matsayin daya daga cikin ma’aikatan fim din, saboda haka ba a haskaka fuskata a cikin fim din ba.
Ko ta yaya ka samu lakabin sunan ‘West’?
A lokacin da na dawo Kano, na zauna na ne a unguwar Birget, inda nake buga wasan kwallon kafa ba kama hannun yaro. A lokacin akwai wani fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya mai suna Taribo West. Ganin yadda nake wasa irin nasa, sai yaran unguwarmu suka fara kirana West. Shi ke nan sunan ya bi ni.
Yawancin kakan fito a matsayin dan ta’adda ko mai tayar da zaune tsaye  a fina-finai, ko me ya sa ka zabi irin wadannan rol din?
Tun kafin shigowata fina-finan Hausa, idan ina kallon fina-finan Indiya, ina sha’awar yadda basawa ke nuna izza da gadara da cin-alwashi da kuma isa. To da Allah ya yi abincina a nan yake, ni ma sai na ce nan bangaren nake sha’awa kuma sai na samu karbuwa a hakan. Amma nakan fito a matsayi wanda ba ya tada zaune tsaye, musamman idan aka duba sababbin fina-finan da nake ciki a yanzu.
Masu karatu za su so su ji dalilin shakuwarka da fitaccen jarumi Ali Nuhu?
Ka san shi dan Adam yana kaunar mai kyautata masa, saboda duk abun da Ali ya ce za ka ga ina rawar jiki zan yi ba tare da wani bata lokaci ba. Ina ganin wannan ne dalilin da ya sa muka shaku. A gaskiya da shi da kuma Adam A Zango mutane ne biyu da ba zan taba mantawa da su a rayuwata ba.
Nasarori
A gaskiya nasarorin da na samu a wannan sana’ar suna da dama, amma wadanda zan tuna da su, su ne: na gina gidaje nawa na kaina akalla guda biyu, ina kuma da motocin hawa akalla guda uku da sauransu. Shi ya sa sai dai mu ce Alhamdulillah.
kalubale
Kodayake muna da yawa da muka fuskanci kalubale a lokacin. Amma hankalina ya tashi sosai a lokacin da wani abu ya faru da wata ’yar uwarmu (Maryam Hiyana) saboda irin yadda mutanen suka dinga kyamarmu, duk inda muka taka sahunmu a lokacin.
Burina
Burina shi ne in faranta wa masoyana rai ta yadda zan ilmantar da su da kuma fadakar da su. Kuma yana da kyawu su fahimci cewa wasa ne, ba da gaske ba ne.  Amma babban burina, bai wuce na taimaka wa mahaifiyata da ’yan uwana da kuma sauran al’umma ba.
Iyali
Ina da mata daya da ’ya’ya biyu.