Malam Shehu wanda aka fi sani da suna Sarkin Mayun Nasarawa ya bayyana wa Aminiya dalilan da suka sa ake kiransa da wannan suna. Kuma ya fadi yadda ya gaji sarautar daga mahaifinsa, wanda shi ma ya gada daga kakansa:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Ni mutumin garin Garkawa ne da ke Jihar Filato, amma asalin tushena daga Jihar Sakkwato ne, garin Kwanni. Dalilin da ya sa nake zaune a garin Lafiya ta Jihar Nasarawa shi ne, mahaifina ya dawo nan ne saboda rigingimun da suke faruwa a Jihar Filato.
A ynan Arewa, idan aka ce wa mutum maye ana rigima, wadansu har kotu suke zuwa don a wanke su, kai yaya kake amsawa?
Eh haka ne, amma ko a nan ana rikici sosai idan an ce wa mutum maye.
Me ya sa ake ce maka Sarkin Mayu, kuma kake kiran kanka da haka?
Dalili shi ne, mahiafina yana bayar da magani, don ya gada daga mahifinsa, don haka na yi gadon gado ke nan. Mahifina yana ba da taimako har ya shahara don haka aka fara kiransa Sarkin Mayu a Jihar Filato. Da muka dawo Lafiya sai ya ci gaba da ba da magani. Sai aka rika ce masa Sarkin Mayun Filato da Nasarawa. Ya bar mini wasiyya cewa in ya rasu in ci gaba da ba da magani. Don ni matashi ne kuma da na shahara sai na fara yin amfani da kafafen yada labaru ina ba da magani. A takaice, idan mutum ya ce yana neman gidan Sarkin Mayu, wurina ake kawo su. Don haka ba na damuwa don an ce mini Sarkin Mayu.
Me ake ce wa mahaifinka da ka gaje shi?
Ana ce masa Sarkin Mayun Garkawa, a taikace mun yi gadon ba da magani ne tun kaka da kakanni.
Mece ce maita?
Maita baiwa ce, wani ana haihuwarsa da ita, wani kuma yana nema har ya samu. Wadansu suna neman maita don su tsare jikinsu sannan wadansu na nema don su cutar da mutane. Ina ba da taimako har a warke daga ciwon maita wato idan an yi wa mutum asiri, har ya samu lafiya. Idan aka kama mutum ina ba da taimako, ina boye kurwa. Akwai abin da ake cirewa idan ba a boye kurwa ba, in an so a yi wa mutum asiri, ba za a gani ba.
Mece ce kurwa?
Asiri ne da muke ganewa ta sihiri, amma muna boye kurwa.
Shin ko ana iya cewa ’yan kungiyar asiri mayu ne?
Ai ’yan kungiyar asiri suna da illa matuka, domin suna son jini da yawa a koyaushe, suna yin asiri a ga mutum, ko a hanya ko a mota sannan a cikin mako guda ya shiga cikin mutum har a kamu da rashin lafiya.
Yaya kake yin aikin cire maita?
Ina kwancewa ko cire maita ta hanyar ba da magunguna iri-iri.
Su wa aka fi jifa da maita ko asiri?
An fi yin jifa tsakanin masu neman sarauta ko mukaman siyasa ko masu son karin girma a ofis.
A ina aka fi jifar mutane?
Iri-iri ne, amma sun hada da na mantuwa da na hanta da sauransu. Akwai matar wani babban basarake da kishiyoyi suka jefe ta, aka kai ta kasashen waje ba a dace ba, da aka kawo mana ita gidana, na yi mata magani.
Idan mutum ya je asibiti aka gwada shi aka ce yana fama da ciwon da ba a gane ba, ana turo maku shi?
Muna da kyakkyawar fahimta da su, ina an kawo mana ciwon da ba namu ba kamar na rashin jini ko ruwa, muna aika musu. Haka su ma idan ba su gane ba suna turo mana
An ce kana yin shari’a, wacce iri shari’a kake yi?
Ina yi idan an turo min daga Fadar Sarki ko daga kotu kan in warware kazafi da aka yi wa wani cewa maye ne, in bincika da gaske ne ko sharri ne da kazafi. Yawanci kuma kazafi ne domin rashin jituwa.
Idan mutum yana da maita, amma ya tuba, in ya zo kana iya cire masa maitar?
Kwarai kuwa. Ina da sana’a don ana yi mini kiwon shanu, amma mahaifina ya ce in tsaya don taimaka wa jama’a kuma ana dacewa.
Sarki ya san da zamanka da wannan suna?
Sarki shi ne uban kasa kuma ya san muna ba da taimako.
Ko an taba yi maka nadi?
Ina da nadi kuma a fada aka yin mini. Akwai Sarkin Magani kuma akwai Sarkin Mayu, muna hada kai don taimakon jama’a.
Su wa suka fi yin maita ko yin asiri da tsafi don su cutar da wani?
Masu neman mukaman siyasa da masu son duniya da masu neman sarauta suna shirka, wani in an jefe shi, ana kawo mana shi bai san inda yake ba. Wani babban basarake da aka jefe shi, idan hakimai ko fadawa sun zo gaishe shi ko sau goma ne, sai ya rika amsawa kamar ya ga bako, wato yana nuna bai san su ba. Matan masu kudi sun fi zuwa don a yi musu shirka, kada a yi musu kishiya ko kuma su zama masu juya miji a kan kishiyoyinsu. Wace shawara za ka bayar game da masu yin maita da tsafi?
A ji tsoron Allah, ba sai an kauce hanya za a samu duniya ba. Masu magani su rika gaskiya, sai a ce mutum maye ne bayan ba ya da ita, ka ga an raba zumunta.
Yaya ’ya’yanka suke ji idan an ce musu ’ya’yan Sarkin Mayu?
’Ya’yana ba su jin haushi, domin ni ma na gaya musu cewa ba na jin haushi lokacin ina yaro.