✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da aka tsare ni – Buba Galadima

A ranar Lahadin makon jiya ne wato kwana guda bayan zaben Shugaban Kasa, labari ya bazo cewa wadansu jami’an tsaro sun yi awon gaba da…

A ranar Lahadin makon jiya ne wato kwana guda bayan zaben Shugaban Kasa, labari ya bazo cewa wadansu jami’an tsaro sun yi awon gaba da Injiniya Buba Galadima kan wasu bayanai da aka ruwaito ya yi kan sakamakon zaben. Sai dai hukumomin tsaro na kasar nan sun musanta cewa su ne suka kama shi. A karon farko bayan bayyanarsa kwana daya da bayyana sakamakon zaben da Hukumar INEC ta yi, jigon na Jam’iyyar PDP ya yi wa Aminya bayani a kan lamarin:

 

Kwatsam, sai ga labarin bacewarka mene ne ya faru?

To ni abin da na dauka shi ne dama irin haka na iya aukuwa, domin idan akwai wani mutum a kasar nan da gwamnati ba ta jindadin  kalamansa ko Jam’iyyar APC ba ta kauna, to na dauki kaina a matsayin  na daya ko na biyu. Saboda haka idan aka taho ana zabe irin wannan, mutane irinmu da ba za su iya ganin zalunci su yi shiru ba, dole sai an boye mu don a samu damar yin abin da ake son yi wanda hakan ya saba ka’ida. A ganina wannan shi ne abin da aka yi, kuma ko ma su wane ne suka aikata, sun samu nasara. Saboda daga lokacin da na bar harabar siyasar nan, abubuwa da yawa sun auku kuma al’umma ba su da damar sani, wanda da ina nan babu abin da zai iya hana ni fadin abin da  ke ciki a zahirance wanda ba farfaganda ba ne kuma ba karya ba.

Sai dai ba na son na zurfafa bayani a kai saboda abin ya shafi mutane da yawa kuma ba na son ya shafi aikinsu, saboda idan na ce har sai na yi bayanin to sai abin da ba a so ya fito. Kuma koma mene ne Najeriya ta fi karfin Buba Galadima, koda Buba ko ba Buba Najeriya za ta ci gaba da wanzuwa. Saboda haka mu yi zance a kan abin da ya shafi Najeriya, me aka yi a lokacin zabe kuma me ake zaton za a yi a kan zaben da ke tafe, sannan mene ne dabarunmu na hana sake aikata irin abin da aka yi mana a lokacin zaben Shugaban Kasa?

A baya kun yi ta hasashen ku ne za ku yi nasara a zaben Shugaban Kasa, sai g ashi an samu akasi, me za ka ce?

Ba a samu akasi ba! Tabbas Allah Ya sani mu ne muka ci zaben nan amma sai aka nuna mana fin karfi da kama-karya da iko na gwamnati ta hanyar amfani da jam’an tsaro ciki har da soja wadanda babu abin da ya shafe su a harkar zabe. Domin Kotun Koli ta yi fatawa a kai tun a baya cewa kada a ga soja a harkar zabe. Kuma mu din nan tare da Janar Muhammadu Buhari ne muka kai kara Kotun Koli ta yi wannan furuci, amma yau sai ga shi a mulkinsa shi da kansa yake sa a yi haka. To duk abin da ka yi wa wani na zalunci ka jira naka yana zuwa. Wani abin mamaki shi ne idan wadanda ke ikirarin sun ci zaben nan suna da yakinin cewa sahihin zabe ne aka yi, sun ci zaben a kan gaskiya, to mene ne tsoronsu da har suke ta kama kafa ga kasashen duniya da manyan mutane a kasar nan da kungiyoyi ana ta zanga-zanga na kada a je kotu?

Dan Adam yana da mantuwa, ko in ce so hana ganin laifi. In ba haka ba shi fa wanda ake cewa kada a kai kararsa zuwa kotu, sau uku yana tsayawa zabe yana faduwa, kuma a duk faduwarsa sai da ya garzaya zuwa kotu. Mun yi wata 60 cir muna zuwa kotu da shi muna neman a bi mana kadin zaluncin da aka yi mana. Shin daidai ne a al’adance ko a Musulunce, kai don an zalunce ka sai ka zalunci wani?  Ni dai a nawa gani ba daidai ba ne. Kuma malaman da suke cewa Atiku Musulmi ne Buhari Musulmi ne, saboda haka kada Atiku ya garzaya kotu, ina ganin suna da mantuwa da son kai. Saboda a lokacin da Buhari ya tsaya takarar zabe da Jonathan a 2015, Jonathan fa suka yi suka karbi kudinsa Naira miliyan 600. Ko don Buharin ya rufa musu asiri ne don sun taimaka masa. Da dai sun goyi bayan Atiku ne a wannan zaben suna da bakin da za su ce kada Atiku ya je kotu, amma ba su goyi bayansa ba, to ina ruwansu, su bar shi ya je in ya so kotun ta ce ba ya da gaskiya.