Ko za mu ji tarihinka?
Sunan Isma’ila Usman ‘Yandaki, Mataimaki na musamman ga Sanata Umaru Ibrahim Kurfi. An haife ni a nan garin ‘Yandaki a shekarar 1986, na yi karatun Firamare a nan ‘Yandaki, sai Sakandire ta Community da ke Kaita kafin a mayar da ita ta kimiya. Daga nan sai na tafi Makarantar Kimiya da fasaha ta Hassan Usman inda na yi karatu a kan Sakatariya. Amma a lokacin ina aji biyar a Firamare, an tura ni Kano wajen karatun kur’ani a Unguwar kofar Nasarawa kusa da gidan Alhaji Abdulmanafi wanda kuma ya bani damar shiga harkokin kasuwanci. Na yi kamar shekara 7 a Kano. A lokacin da ina Kano na shaku da gidan Alhaji Abdulmanafi wanda hakan ya bani damar shiga cikin harkokin gidansu da suka bude a nan Katsina. Na fara daga mai matsa mai har zuwa manaja. Har ta kai ina sayo man da kaina ina sayar wa bayan na kama wani gidan ne domin ci gaba da wannan harka wadda nake ciki har yanzu. Kazalika na shiga cikin harkokin siyasa, na fara shiga cikin masu jagoranci a mazabata ta ‘Yandaki tun daga jam’iyyar APP a matsayin sakataren kudi, har aka zo ANPP har zuwa CPC. Kuma na zamo shugaban sauran shugabannin jam’iyar na karamar Hukumar Kaita. Na zamo Mataimaki na musamman na danmajalisa mai wakiltar Kaita da Jibiya a 2011 har zuwa 2015. Kafin zaben 2015 na zamo daya daga cikin shugabannin jam’iyyar, wato ‘Ed-officio 1’ har zuwa yanzu. Ina iya cewa wannan dalili na daga cikin dalilan da suka sa Sanata Umaru Kurfi ya bani Mataimaki na musamman.
Ya aka yi ka samu sarautar gargajiya?
To kasan duk abin da mutun yake yi a rayuwa, akwai wasu na can gefe suna kallonsa. To a karamar Hukumar Kaita na san an yi ‘yan siyasa iri-iri tare da mukamai daban-daban, amma a batun mataimaki na musamman ga wani Sanata, ba a taba samu ba. Kuma tun daga jam’iyyar CPC har zuwa yau duk wani aikin da za a kawo karamar Hukumar nan, ni ke jagorantar kawo shi. To wannan ne ya sa shi Mai girma Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin Kaita ya kara sa ido a kaina ba tare da na sani ba. Ana cikin haka sai Allah Ya jarabci garin Kaita da wani iftala’i na rushewar gidaje tare da lalacewar na’urar taransifomomi. Sai na jagoranci shi Sanata Umar Kurfi ya zo ya jajanta wa wadanda suka samu wannan jarabawa a nan fadar Hakimi, sannan kuma ya ce duk gidan da ya rushe ya bada naira dubu 20 a matsayin gudunmuwa. An kuma ba duk wanda abin ya shafa tare da biyan kudin gyaran ita taransifomar. To a wajen jawabin godiya da shi Hakimi ya yi, bayan ya kara shaida wa Sanata cewa ga amanata nan ya ba shi, sai ya ce ya ba ni Garkuwan Kaita. Da ma Allah Ya yi wa mai rike da wannan sarauta na farko rasuwa.
Mene ne aikin ita wannan sarauta?
Aikin wannan sarauta ya hada da cewa kana cikin ‘yan majalisar Hakimi. Kuma kamar yadda kowa ya sani, shi Garkuwa ko a fagen yaki an san wanene. Farko dai kariya ce ga sarki daga harin mahara. Sannan kuma shi ke kare duk wani abin da zai cutar da masarauta da sauran irinsu. To abin da ake nufi shi ne, duk wani abin da zai cutar da karamar Hukumar Kaita ni ne zan nemo yadda za a kare shi. To yanzu da yake ba lokacin yaki bane sai aikin ya canza salo. Sai ya zama shi ne mai kokarin kawo cigaba a masarautar bayan kariya
Ya ka ji da aka nada ka wannan sarauta?
Abu na farko dai da na ji shi ne na dauka wannan yabo ne aka yi mani na irin yadda aka ga kokari na na kawo cigaba a karamar Hukumar baki daya ba wai ga masarauta ba kadai. Wannan ya zamo abin alfahari a gare ni tare da jin dadi. karin jin dadin shi ne an bani ita ba tare da na san za a bani ba.
Mun samu labarin kana da wata sarautar?
Ba ita kadai ba ce. A lokacin da Galadiman ‘Yandaki Alhaji Yazid ya ji labarin cewa an ba ni Garkuwan Kaita sai ya ce ai shi ne ma ya kamata ya fara sanar da ni kudurinsa na ba ni wata sarauta a garin da aka haife ni. Domin ba wai cika baki ba, a batun kawo cigaba a garin’ Yandaki musamman ta fuskar siyasa, gaskiyar magana ba ni da na biyu. Domin ko da zabar mutun aka yi a siyasance na tabbata bai yi wa ‘Yandaki abin da na yi ba. Kuma su mutanen ‘Yandaki sun shaida mani cewa sun san ina da halin da zan iya zama ko Landan ne, amma ina nan cikin garin tare da su kuma ana yin komai tare da ni. Sannan wani abin da suke kara alfahari da shi shi ne ni na fara tsayawa tsayin daka har aka samu rijiyar burtsatse ta farko wadda ta kawo ruwa cikin garin. Maganar gyara kuwa in matsala ta samu rijiyoyinn, ni nake yin gyaran, mutanen garin kuma sun san haka. Sannan akwai batun jarabawa ta daliban makarantar jeka-ka-dawo ta nan cikin garin, bai wuce mako biyu a rufe rajistar ba, ga shi makarantar ba su yi rajistar ba har ya rage mako daya. Amma cikin ikon Allah lokacin da ‘yan kwamitin suka kira ni suka shaida mani, Allah Ya taimaka na yi wa Sanata waya, cikin awa 2 ya turo da kudin aka je aka bude wannan santa ta wannan makaranta. Ina alfahari da mahaifata kuma ina yi wa Allah godiya da yake ba ni damar bayar da gudunmuwa ta don ci gaban garin. To wadannan abubuwa na daga cikin dalilan da suka sanya shi Galadima ya kalla kamar yadda mahaifinsa ya kalli wadancan, shi ma ya ce daga gida ya kamata a fara, saboda haka ya ba ni sarautar Magayakin ‘Yandaki, kuma ni ne na samu wannan sarautar a karkashin Galadiman ‘Yandaki. Ita dai wannan sarauta ba sai na yi dogon bayani a kanta ba, saboda an san yadda take tun zamani mai tsawo. Ita a yanzu tunda ba yakin ake yi ba, sai in ce ta koma kamar waccan ce ta Garkuwa. Ma’ana, na zamo kamar fitila ko madubin da zan hango wani abu na alheri ko akasi tun daga matakin mahaifata har ya zuwa ga masarautar baki daya har zuwa ga matakin karamar Hukuma. Sannan kuma ni zan bi hanyoyin da suka dace domin kawo abin ko kuma kawar da shi a gargajiyance ba kawai a siyasance ba.
Ke nan siyasa ta taka muhimmiyar rawa wajen samun sarautar da ka yi?
Wannan haka ne. Kuma haka ya kamata a ce duk wani dan siyasa ko mai ra’ayin siyasa ya kasance. Ka zamo mai kokarin kawo wa al’ummar cigaba ba nakasa su ba. Ka zamo kana tare da jama’ar komai wuya ko dadi. Ba wai sai lokacin da kake neman goyon bayansu ba. Kuma bari in fada maka wani abu, ita kanta siyasar ba wai na shige ta bane haka nan, sai da na lura da irin yadda ‘yan siyasar suke shigowa wajenmu suna yi mana romon baki, amma da zarar sun samu biyan bukata ba mu sake ganinsu. Ni kuma Allah Ya sani bani son abin da zai kawo wa jama’ata nakasu ko makwabtana.
An ce kai ne mutun na farko da aka yi wa nadin sarauta biyu a rana guda a wannan masarauta?
Haka ne. Hakika ni ne mutun na farko kuma matashi wanda ba wai a masarautar Sarkin Sullubawan Katsina Hakimin Kaita ba, ina iya cewa a masarautar Katsina baki daya ni ne wanda aka taba yi wa irin wannan nadi. Kuma wani abin ban sha’awa shi ne yadda dukkan mukaman suka fito a tsakanin da da uba, an kuma nada ni a ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar 2017. Sarautar Magayaki Galadiman ‘Yandaki Alhaji Bello Abdulkarim ya fara nada wa a garin na ‘Yandaki, sannan kuma daga nan sai fadar Maigirma Sarkin Sullubawan Alhaji Abdulkarim Kabir Usman da ke cikin garin Kaita inda ya nada ni Garkuwan Kaita.
A matsayinka na matashi dan siyasa baka ganin wannan wani kalubale ne gare ka?
To Hausawa na cewa mai kamar zuwa a kan aika. Farko dai duk da ina dan siyasa ban taba rike wani ofis wanda zance jama’a sun zabe ni a kan shi ba, duk mukamin da na rike ko nake rike da shi ta fuskar siyasa ba na zaben jefa kuri’a bane. Don haka a nan ina iya cewa wannan sarauta kamar wata allura ce wadda za ta kara zaburar da ni wajen ci gaba da aikin da nake yi
Ko kana da sha’awar tsayawa takarar siyasa?
To wannan tambayar taka sai in ce lokaci ne zai bayar da amsarta. Amma duk da haka, sanin kowa ne cewa duk inda dan siyasa yake, matsawar ya kai ga wani fage a siyasar to ba zai rasa wani kuduri ko sha’awar wani abu ta fuskar siyasar ba. Ni ma kuwa ba zan fidda kaina daga cikin irin hakan ba. Amma dai kamar yadda na fada, lokaci tare da jama’a ne za su amsa wannan tambaya.
To yanzu wane fata ko kira ke gare ka?
To zan fara da yin kira ne ga al’umma musamman masu hali da ‘yan siyasa. Mu sani duk abin da Allah Ya mallaka mana, ya bamu ne domin mu taimaki wadanda ba su da shi. Masu siyasa su sani ba a yin ta sai kana da jama’a, su kuma jama’a kana samunsu ne in kana tare da su. Mu rage yin alkawalin da muka san ba za mu iya cika shi ba. Sannan a matsayina na mai kananan shekaru, ina kira ga jama’a ta da su rika sanya ni hanya a duk inda suka ga na kauce. A karshe ina godiya ga Masarautar Kaita da ta Sarkin Katsina baki daya domin sai da ta amince sannan aka bani wadannan sarautu. Allah Ya cigaba da shige mana gama.