An mayar da maki 15 da aka zaftare wa Juventus a Serie A, bayan da wata kotun sauraron kararrakin wasanni ta yi umarnin a sake bibiyar laifin da ake zargin kungiyar.
A watan Janairun 2023 aka hukunta Juventus, bayan da aka sami kungiyar da laifin bayar da bayanan karya na hada-hadar kungiyar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabbin Ma’aurata Suka Yi Azumin Farko A Najeriya
- Sallah: DSS ta gargadi al’umma bayan kama bindigogi a Kano
Da wannan hukuncin Juventus ta koma ta uku a teburin Serie A, amma za a iya sake hukuntata idan an sameta da laifin bayan bibiyar zargin da ake mata.
Daraktan Tottenham, Fabio Paratici bai yi nasara kan daukaka karar da ya shigar ba, wanda aka dakatar wata 30, kan laifin da ake zargin Juventus.
Tsohon daraktan wasannin Juventus, Paratici daya ne daga daraktoci 11 daga kungiyar ta Italiya da aka hukunta.
Ya ajiye aikin da yake yi a Tottenham, bayan da aka fadada hukuncinsa na dakatarwa a fanni tamaula a fadin duniya ba iya Italiya ba.
Lamarin ya faru ne a lokacin da kungiyar Arewacin Landan ke neman kociyan da zai maye gurbin Antonio Conte, bayan da suka raba gari.
Kamar yadda aka yi watsi da daukaka kakar Paratici, an kuma ki amincewa da daukaka karar da tsohon shugaba, Andrea Agnelli da babban jami’i, Maurizio Arrivabene da daraktan wasanni, Federico Cherubini da suka shigar.
Tsohon darakta, Pavel Nedved da Paolo Garimberti da kuma Enrico Vellano sun yi nasara a daukaka karar da suka shigar.
Yanzu kotun hukumar kwallon kafar Italiya za ta sake bin bahasin zargin da ake yi wa Juventus, wadda ita ta yanke hukuncin farko na kwashe maki 15 daga kungiyar.
Saura wasa takwas a karkare gasar Serie A, kenan Juventus ta mayar da AC Milan mataki na biyar, a teburi ita kuwa Roma ta koma ta hudu a babbar gasar tamaula ta Italiya.