✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar fim harka ce ta malanta —Saratu Zazzau

Saratu Abubakar Zazzau, ’yar wasan kwaikwayo a harkar fina-finai ta Kannywood, ta ce a yanzu al’umma ta fahimci cewa ‘yan fim maamai be don haka…

Saratu Abubakar Zazzau, ’yar wasan kwaikwayo a harkar fina-finai ta Kannywood, ta ce a yanzu al’umma ta fahimci cewa ‘yan fim maamai be don haka ta daina kyamar su.

“Ai dan fim kamar kowa ne; dan fim malami ne, saboda fim malanta ce [mai] zaman kanta saboda tana koyar da abubuwa na tarbiyya, da zaman aure….”, inji ta.

Saratu, wacce ta shafe fiye da shekara 20 a masana’antar ta Kannywood, tauraronta ya haskaka ne bayan fitowar da ta yi a cikin shirin nan mai dogon zango na “Kwana Casa’in”.

A cikin shirin, jarumar ta fito a matsayin Shugabar Makarantar Dokta Juwairiya Grema, lamarin da ya sanya hatta a wajen shirin ake mata lakabi da suna Dokta Juwairiya ko kuma Principal.

Jarumar ta ce a halin yanzu babu gidan da ba a mu’amala da ‘yan wasan kwaikwayo, saboda akwai bangarori da dama, kamar waka da daukar hoto da kuma fitila da kwalliya da sauransu.

“‘Yan fim na fadakarwa”

Dokta Juwairiya Grema ta ce, “Ina kira ga jama’a da su daina kallon ‘yan wasan kwaikwayo a matsayin mutanen banza, saboda fadakarwa da wayar da kai da suke yi a tsakanin al’umma.

“Saboda haka dan wasan kwaikwayo tamkar malami ne domin yana fahimtar da al’umma ne.

“A gaskiya tun da na taso ina son wasannin kwaikwayo, musamman wasan Hausa.

“Haka ni Allah ya yi ni dalilin haka ne bayan kammala makaranta na shiga harkar rawar koroso na tsawon shekara uku, kafin na shiga harkar wasan kwaikwayo gadan-gadan a shekarar 2002.

 “Na shiga wasanni daban-daban, amma wannan shirin da na fito a matsayin Shugabar Makarantar Grema, wato “Kwana Casa’in”, shi ne babban shirin da ya fito da ni aka san ni sosai.

“Kwana Casa’in”

“Na samu shiga shirin ne ta hanyar wani dan uwana da ke mu’amala da su wanda ta hanyarsa ne na shiga gwajin da aka yi mana kusan mu 35 zuwa 40.

“Sai bayan kwana uku suka fidda sakamakon cewa na yi nasara domin a cewarsu na cika dukkan ka’idojin da ake bukata.

“A sakamakon da aka fitar ne aka tabbatar da cewa ni na yi nasara a wannan fannin da ake bukata a cikin shirin.

’Yan fim malamai ne masu koyar da tarbiyya, inji Saratu Zazzau