✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin Buhari na jingine batun janye tallafin man fetur

Za mu koma mu yi wa Kasafin Kudin bana kwaskwarima.

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da jingine batun zame hannunta dungurungum daga biyan tallafin man fetur da a baya ta ayyana cewa zai soma aiki kai tsaye a watan Yulin bana.

Ministar Kudi, Kasafi Da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed ce ta bayyana hakan a jiya Litinin a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke tararrabi kan yiwuwar kara farashin man da zai kara tsananta rayuwarsu ta yau da kullum doriya a kan wadda ake fuskanta.

A wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya jagoranta, Ministar ta ce jingine batun janye tallafin ne ya sanya dole Majalisar Zartarwa ta kasa ta sake waiwaye kan Kasafin Kudin Kasar na bana domin yi masa kwaskwarima.

Ministar ta ce gwamnati ta sake nazari ne a kan matakin da ta shirya dauka, bayan amincewa da Kasafin Kudin shekarar 2022, lamarin da ta ce an yi kuskure wajen zabar lokacin zartas da matakin janye tallafin mai kwata kwata.

A cewarta, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gwamnati ta yanke shawarar ba za ta aiwatar da matakin ba, la’akari da hasashen cewa ’yan Najeriya na fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki, kuma cire tallafin zai kara dagula lamarin tare da kara jefa jama’a cikin karin kunci.

A baya dai gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar an yi tanadin biyan kudin tallafin man fetur ne daga Janairu zuwa Yuni kadai, abinda ke nufin daga watan Yuli za a cire tallafin baki daya.

Babu shaka an shiga zaman zulumi a Najeriya tun bayan da batun janye tallafin man fetur ya bulla, inda har ta kai ga Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta kudiri aniyar gudanar da zanga-zangar a duk sassan kasar a ranar 27 ga watan Janairu da kuma 1 ga watan Fabrairun bana.

Tun a karshen shekarar da ta gabata ce ruwayoyi ke cewa za a janye tallafin, har ta kai ga gidajen mai da dama suka yi ta tsimi da tanadin man da suke sayarwa a manyan biranen kasar, ciki har da Abuja babban birnin kasar.

Wani abin da ya karfafa zaton janye tallafin shi ne rashin sanya tallafin a cikin kasafin kudin kasar na bana, wanda a yanzu Ministar Kudin ta kawar da shakku da cewa akwai tanadin tallafin man fetur din a cikin kasafin tun daga farkon wannan shekara har zuwa watan Yuni, lamarin da ya sanya ta ce za a yi wa kasafin kudin kwaskwarima.

A makon jiya ne da Majalisar Tattalin Arziki ta kasa (NEC) ta gudanar da taronta, an yi tsammani za ta fadi ainihin matsayar gwamnati game da janye tallafin, amma sai ta ce ’yan majalisar ba su bijiro da batun tallafin man fetur din ba a yayin taro kuma ba a yanke wata shawara a kan wannan maganar ba.

Haka zalika, tsohon Shugaban Najeriya a zamanin Mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar, ya ja kunnen Gwamnatin Tarayya cewa a kul idan ta janye tallafin fetur, har man fetur din ya kasa tsada, to za a kara jefa ’yan Najeriya cikin matsin da ya fi wanda su ke ciki a yanzu.

Tsohon Shugaban Kasar ya yi jawabin ne a wurin Taron shekara-shekara karo na 19 da Kamfanin Jaridar Daily Trust ya gudanar a ranar 19 ga Janairu, a Abuja, kan maudu’in “Zaben 2023: Siyasa, Tattalin Arziki Da Matsalar Tsaro.”

Ko a karshen makon nan da ya gabata, Kungiyar Kwadagon Najeriya ta TUC ta gindayawa gwamnatin Najeriya sharuddan da ta ce dole ta kiyaye kafin aiwatar da shirinta na cire tallafin man fetur nan da ‘yan watanni.

Bayan taron da ta yi a ranar Asabar TUC ta zayyana tabbatar da gyara dukkanin matatun man Najeriya da fara aikinsu, da kuma wadata al’ummar kasar da abinci kan farashi mai rahusa da samar da ababen more rayuwa, a matsayin sharuddan da ta gindaya wa gwamnatin kasar.

Tun cikin watan Nuwamban da ya gabata, Ministar Kudin ta bayyana shirin cire tallafin man fetur, wanda ta ce za a maye gurbinsa da bayar da tallafin sufuri na naira dubu biyar ga masu karamin karfi akalla miliyan 40, domin rage musu radadin tasirin da matakin zai haifar.