✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilan dakatar da hakar ma’adanai a Zamfara’

A karshen makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara, bayan da ta zargi masu gudanar da harkar da rura wutar…

A karshen makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara, bayan da ta zargi masu gudanar da harkar da rura wutar kashe-kashen da ke gudana a jihar,  jim kadan da bayyana wani sabon shirin yaki da ’yan bindiga a wasu jihohin kasar nan mai suna Operation Puff Adder “Shirin Farmakin Kasa”.

Mutane sun rika mamaki kan dalilin da gwamnati ta jingina batun hare-haren ’yan bindigar da hakar ma’adanan.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa su kansu wuraren hakar ma’adanan ba su tsira daga hare-haren ’yan bindiga a Jihar Zamfara ba, misali a cikin watan Janairu bana ’yan bindigar sun kai hari a wani wurin hakar zinare da ake kira Gonar Hajiya a Gundumar Kawaye da a Karamar Hukumar Anka. “Maharan sun sha zuwa Gonar Hajiya su yi garkuwa da masu hakar zinare, su kuma yi fashin kudi da zinaren da aka tono a wurin. Wani lokaci ma sukan yi kisan gilla a kan jama’ar da da suka tarar a wurin,” inji wani Shugaban ’Yan Sa-kai, Akilu Damina

Wannan lamari ya fusata wadansu masu hakar zinare, har suka yanke shawarar mayar da martani kan ’yan bindigar, kuma ana cikin haka ne wani lokaci ’yan bindigar suka kai hari wurin, masu hakar zinaren suka kama daya daga cikinsu suka kashe suka tafi da bindigarsa da babur dinsa. “Matakin da mahaka zinaren suka dauka ya sa maharan suka sha alwashin ramuwar gayya. Don haka suka kai hari a kan kauyen Kawaye suka kashe mutum 13, suka yi garkuwa da wadansu 35. ’Yan bindigar sun yi zargin cewa masu hakar zinare sun zo ne daga kauyen Kawaye, don haka suka kai harin ramuwar gayya kan kauyen,” inji shi.

A Nuwamban shekarar 2016 ’yan bindigar sun kashe mutum 42 a wani wurin hakar zinare da ke kauyen Bindin a Karamar Hukumar Maru. Wani mai aikin zinare mai suna Ali Tukur ya shaida wa Aminiya yadda ya tsira daga wani hari da ’yan bindigar suka kai a mahakar zinare ta Duza a Karamar Hukumar Anka. “Ina barci bayan na yi aiki na gaji, sai na ji wani ya taka min kafafu, ashe yana so ya gudu ne daga harin da aka kawo a wurin da dare. Sai na tashi da sauri kawai na ga mutane da bakaken kaya dauke bindigogi sun mamaye wurin. Da na fahimci an kawo mana hari ne sai na tayar da da abokina da ke barci a kan wata babbar tabarma. Na rada masa cewa an kawo mana hari nan take muka fahimci muna cikin matsala,” inji shi.

Ya ce “Sun kawo harin ne da misalin karfe 11:30 na dare a kan babura, sun sauka daga baburan kamar kilomita daya, suka tako a kafa suka zo wurin hakar zinaren. Sa’ar da suka shigo sun iske wani yana barci sai suka tayar da shi suka ce ya nuna musu dillalan zinaren. Lokacin da suke zagayawa wuri- wuri suna karbar zinare da kudi, sai wani ya yi ihu, inda suka bindige shi. Daga nan suka rika harba bindigogi sama, masu hakar zinare suka gudu cikin daji aka bar zinare da kudadensu a wurin,” inji shi.

Wani mai hakar zinare mai suna Kabiru Atanka ya shaida wa wakilinmu cewa: “Wani lokaci maharan sukan zo wurin hakar zinare amma su tafi ba tare da sun yi wa kowa komai ba. Sukan zo neman tabar wiwi da wasu kayan maye. Wani lokaci kuma sukan aiko yaransu a saya musu tabar wiwi da sigari domin kai masu cikin daji.”

Ya ce barayin sun fara zuwa wurin hakar zinare ne lokacin da suka lura cewa masu aikin zinare da dillalansa suna samun kudi masu yawa, kuma wadansu dillalan suna zuwa wurin daga kasashe makwabta.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun taba kokarin yin fashi a wani wurin hakar zinare da ke kauyen Tungar Daji, sai dai ba su yi ta’asar ba, bayan da aka sasanta a tsakaninsu da mahaka zinaren kuma suka karbi kudi suka tafi.

Wani mazaunin kauyen Kawaye mai suna Murtala ya shaida wa wakilinmu cewa akwai wuraren hakar zinare goma da suka hada da Kawaye da Mai Galma da Bagega da Dadin Kowa da Duhuwa da Duza da kuma Tungar Daji. “To amma, wadanda aka fi hada-hada su ne Duza da Mai Galma kuma su ne wadanda ’yan bindigar suka fi mai da hankali a kansu, suna yawan kai hari wurin suna fashi da kuma sauran ayyukan ta’adanci,”inji shi.

Shugaban Karamar Hukumar Anka, Alhaji Mustapha Gado, ya ce sun dade suna zargin akwai alaka a tsakanin ’yan bindigar da mahaka zinaren da ke ayyukansu a karamar hukumar. “Ta yaya za a ce wadannan ’yan bindiga suna zuwa suna kai hare-haren rashin imani a kauyukan da ke wurin amma sun kyale kamfanonin hakar zinare wadanda a cikin dajin suke? Ba mu taba jin cewa an yi musu wani abu ba. Dama mun riga mun rubuta wa gwamnati wasika muna neman hukumomi su dakatar da ayyukansu, kuma sai ga shi Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin dakatar da su, mun yi marhabin da haka,” inji shi. Kwamishinan Kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu na Jihar Zamfara, Alhaji Bello Dankande Gamji ya nanata matsayinsu ga Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu wanda ya ziyarci jihar na a kori masu hakar zinaren. “Babu yadda za a yi a ce ’yan bindiga na kyale masu tu’ammali da kudi ko kayan kudi sannan su je su kashe mutane a kauye wadanda kananan manoma ne kuma su sace musu dabbobi, don haka matakin korarsu ya yi daidai,” inji shi.

To sai dai Alhaji Shamsuddeen Sani Dahiru, mai kamfanin hakar zinare na ‘Inta General Enterprise’ ya shaida wa wakilinmu cewa suna goyon bayan duk wani mataki na hana ayyukan ta’addanci a jihar, amma ba su jin dadin yadda ake kokarin alakanta hakar zinare da ayyukan ’yan bindigar ba. “Babu wata alaka a tsakanin masu hakar zinare da ’yan ta’addan kuma babu wani abu da muke yi don taimaka musu, mu masu bin doka ne kuma za mu bi doka,” inji shi.

A ziyarar da ya kai Jihar Zamfara a ranar Talata, Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kare matakin da gwamnati ta dauka yana mai cewa sun kori masu hakar zinaren ne don su katse hulda a tsakanin ’yan ta’adda a daji da masu taimaka musu a cikin garuruwa. Ya ce, ’yan sanda za su dauki karin matakai masu karfi a yaki da ’yan bindigar, tare da yaba wa gwamnatin jihar kan samar da yanayin da jami’an tsaro za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a jihar.

A jawabin Gwamnan Jihar Abdul’azeez Yari ya ce mutum dubu uku da 526 ne ’yan bindiga suka kashe a jihar a shekara biyar. Gwamnan wanda ya bayyana haka a taron ganawa da jama’a da Sufeto Janar din ya halarta, ya ce kusan kauyuka 500 aka tarwatsa yayin da aka raunata mutum dubu 8 da 219, kuma wadansu daga cikinsu har yanzu suna nan rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abdullahi Shinkafi ya wakilta ya ce filin noma mai girman hekta dubu 13 aka lalata ko aka yi watsi da shi, saboda manoma sun daina nomansa sakamakon ayyukan ’yan bindigar. Ya ce ayyukan ’yan bindigar sun yi illa sosai ga jihar inda aka lalata dubban shaguna da tilasta dubban jama’a gudun hijira.

Gwamnan ya ce wajibi ne a tabbatar an aiwatar da umarnin dakatar da hakar ma’adanai a jihar sau-da-kafa.

 

‘A zakulo masu daukar nauyinsu a hukunta su’

Daga Adam Umar, Abuja

Wani masanin tsaro a Abuja, Malam Almustafa Liman ya ce shirin yakar ’yan ta’addan Jihar Zamfara da jihohin Arewa maso yamma da sojoji da sauran jami’an tsaro ke gudanarwa a dazuzzukan yankin a yanzu ba zai samu nasara ba sai an fadada shi zuwa zakulo masu daukar nauyinsu ta hanyar samar musu da kudi da makamai da kariya, wadanda ya ce suna cikin al’umma a kauyuka da birane.

Malam Almustafa Liman ya ce matsalolin rashin aikin yi da talauci da siyasa da sayar da kwaya da rashin tsaro a kan iyakokin kasar nan na daga cikin abubuwan da suka jawo fitinar. Ya ce ko jami’an tsaron sun samu nasarar hallaka wadanda ke cikin dazuzzukan, wadanda ke daukar nauyinsu za su sake daukar wadansu sababbin ’yan aiki, saboda haka ya bukaci gwamnatin da ta dora wa jami’an tsaro na sirri alhakin zakulo ire-iren miyagun mutanen da ke daukar nauyinsu ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

Kuma ya bukaci gwamnati ta rika sirranta abubuwan da ta tsara yi kafin aiwatar da su, saboda hakan na bai wa masu laifin damar kara yin damara ko sulalewa, inda ya ce kamata ya yi a ga sakamakon nasarar aikin kawai bayan aiwatar da shi. “Yakar ta’addanci bai tsaya a kashe ’yan ta’addan da ke cikin dazuzzuka ba, sai an hada da masu daukar nauyinsu, saboda wadancan leburori ne kawai, wadanda suka fi cin gajiyar abin ba sa cikinsu, kuma a shirye suke su sake daukar wadanda suka fi wadancan yawa da karfi idan aka kashe wadanda suke yi masu aikin a yanzu,” inji shi.

Game da hana hakar ma’adinai a Jihar Zamfara, masanin ya yaba da haka inda ya ce masu ayyukan laifi sau da dama na fakewa da wani aiki don aikata wani mummunan abu kamar safaran makamai da makamantansu. Kuma ya ce wadansu na iya ta da tarzoma a wuraren da ke da dukiya a karkashin kasa don mutanen yankunan su bar musu wajen kamar yadda ya ce ya faru a wasu yankunan duniya da ke da arzikin ma’adinai. “Dole gwamnati ta rufe ido ta yi abin da ya dace koda wane ne zai shafa. Saboda kullum bayanan sirri na zuwa teburin shugabanni daga kan Gwamna zuwa Shugaban Kasa, dole ne gwamnati ta tsaya ta yi nazari a kan bayanan nan tare da daukar mataki cikin hanzari koda wane ne abin ya shafa,” inji shi.

 

Dukkanmu aiki daya muke yi – Hedkwatar Tsaro

Daga Ronald Mutum da Ibrahim Babangida Surajo

Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta ba da tabbacin cewa babu wani rudani ko matsala a tsakanin rundunoni daban-daban da suke aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma don kakkabe masu garkuwa da mutane da mahara.

Kakakin Hedikwatar Tsaron, Kanar Onyema Nwachukwu ya shaida wa Aminiya cewa babu wani rudu ko rashin fahimta a tsakanin rundunoni daban-daban na tsaro da suke aikin, inda ya ba da tabbacin cewa kowace runduna tana a kan bakanta.

Bayan shirye-shirye da dama da suke akwai, hukumomin tsaro sun sake karo wasu shirye-shirye da za su yi aiki fadada-da-kafada da wadanda ake da su.

Nwachukwu ya ce Shirin Operation Sharan Daji na Hedikwatar Tsaro yana aiki kafada da kafada da Shirin Harbin Kunama na Rundunar Sojin Kasa.Ya ce Rundunar Sojin Sama tana da nata shirin mai suna Operation Tsabtar Daji sai kuma wanda Hedkwatar ’Yan sanda ta kaddamar na Operation Puff Adder, wadanda ya ce duka suna aiki da juna.

Ya ce dukkan shirye-shiryen aikinsu shi ne tabbatar da an kawar da matsalar tsaro daga yankin Arewa maso Yamma.

A ranar 5 ga Afrilu ne Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kaddamar da Operation Puff Adder

a garin Katari da ke Gundumar Bishin a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ya ce zai kunshi sojoji da sauran jami’an tsaro kuma shirin ya kunshi kwararrun jami’ai da suka fito daga hukumomin tsaro masu kaki da fararen kaya masu hazaka da kuma kayan aiki na zamani don a cimma nasarar dakile miyagun ayyukan da suke faruwa a hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma jihohin Kogi da Katsina da Neja da kuma Zamfara.

Shugaban’Yan sandan ya yi kira ga jama’a musamman sarakuna dashugabannin addinai da kungiyoyin matasa da ’yan kasuwa da sauran ma’aikata su taimaka wajen yaki da masu laifuffuka musamman garkuwa da mutane da fashi da makami da barayin shanu da sauran baragurbi.