✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilan da kotu ta bai wa Gawuna Kano

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotun a matsayin zalunci, don haka za ta ɗaukaka kara

A ranar Laraba ce Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Jihar Kano ta yanke hukunci kan karar da Jam’iyyar APC da dan takararta, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna suka shigar suna neman soke nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) na Jam’iyyar NNPP ya samu.

Yayin da dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam’iyyar APC Iya Mashal Sadik Abubakar da jam’iyyarsa suka kalubalanci nasarar da Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed na Jam’iyyar PDP ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan Jihar Kano dai ta soke nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf, a matsayin halattaccen Gwamnan Jihar, inda ta bayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halattaccen wanda ya ci zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris din 2023.

Jam’iyyar APC ce ta shigar da karar a gaban kotun, tana kalubalantar nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf, inda ta yi zargin jam’iyyarsa ta yi aringizon kuri’a da sauran zarge-zarge.

Mai shari’a Oluyemi AkintanOsadebay, ita ce Shugabar Kotun da ta jagoranci alkalan kotun uku wajen yanke hukuncin.

Dalilin da kotun ta bayar na sauke Abba Kabir Yusuf daga kujerar Gwamna shi ne samun sa da jam’iyyarsa ta NNPP da laifin ringizon kuri’a dubu 165 da 633, wadanda aka gano ba su da hatimi da kuma kwanan wata a jikinsu.

Alkalan Kotun sun kuma bayyana cewa babu sunan Abba a rajistar ’ya’yan Jam’iyyar NNPP ta da bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), don haka bai cancanci tsayawa takara a karkashin inuwar jam’iyyar ba.

Tun farko a watan Maris 2023, Hukumar INEC ta ce dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaben ne da ratar kuri’a dubu 128 da 900 a kan takarar APC, Nasiru Gawuna.

A cewar Hukumar INEC, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya samu kuri’u mafiya rinjaye da suka kai miliyan daya da dubu 19 da 602, inda Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ke biye da shi da kuri’a dubu 890 da 705.

Sai dai bayan da masu kara suka gabatar wa kotun cewa akwai jabun kuri’u kuma da aka tantance sai kotun ta amince ta cire kuri’un bogin inda kuri’un Jam’iyyar NNPP da Abba suka koma dubu 853 da 939, yayin da APC da Gawuna suke da kuri’a dubu 890 da 705, wanda hakan ya sa Gawuna da APC suka zarce Abba da NNPP da kuri’a dubu 36 da 766.

Don haka sai kotun ta umarci
Hukumar INEC ta soke takardar shaidar cin zaben da ta ba Abba, kuma ta bai wa Gawuna takardar lashe zaben.

Alhaji Nasiru Gawuna da Jam’iyyar APC sun shigar da kara ne suna neman a soke zaben Abba bisa zargin cewa ya tsaya takara alhali sunansa ba ya cikin rajistar ’ya’yan Jam’iyyar NNPP.

Sun kuma yi zargin an tafka magudi a wasu rumfuna masu kuri’u 130,000, wadanda idan aka soke rumfunan, su suke da kuri’u mafiya rinjaye.

Alkalan sun karanto hukuncin kotun da kuma yanke hukunci ne ta Manhajar Zoom duk da matakan tsaron da aka dauka a harabar kotun da ke Titin Miller a birnin Kano.

Amma lauyoyi da wakilan jam’iyyun da lamarin ya shafa sun kasance zaune a cikin kotun inda suka saurari yanke hukuncin ta hanyar Intanet.

Har aka kammala yanke hukuncin babu wani bayani kan dalilan da suka hana alkalan halartar zaman kotun da kansu.

Sai dai kafin ranar yanke hukuncin al’amuran siyasa sun yi zafi a tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun biyu na APC da NNPP a jihar.

Idan za a iya tunawa a baya
babbar mai jagorantar shari’ar ta koka kan yadda wasu ke yunkurin bai wa alkalan cin hanci domin samun nasara.

A hukuncin farko da kotun ta fara yankewa ta yi watsi da bukatar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir da Jam’iyyar NNPP da kuma Hukumar INEC suka shigar na bukatar a kori karar da Jam’iyyar APC ta shigar.

Hakazalika kotun ta kori karar Jam’iyyar APC cewa bai dace Abba ya yi takarar ba, domin shi ba dan Jam’iyyar NNPP ba ne, kuma babu sunansa a jerin ’ya’yan jam’iyyar.

Alkalan kotun sun sanar da cewa batun takara al’amari ne na cikin gidan jam’iyya, don haka bai shafi masu kara ba, ballantana su tsoma baki a ciki.

Jam’iyyar APC da Gawuna na korafin cewa Abba Kabir Yusuf ba cikakken dan Jam’iyyar NNPP ba ne, kuma ba ya cikin rajistarta a lokacin da ta tsayar da shi takara, don haka bai halatta ya yi takara ba.

Haka daya abin da Jam’iyyar APC take korafi a kai shi ne zargin magudin zabe da ya shafi kuri’a dubu 130 wadanda a cewarta, idan aka soke su, dan takararta Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ne zai zana wanda ya ci halattaccen zabe.

NNPP za ta daukaka kara

Jam’iyyar NNPP ta yi fatali da hukuncin da kotun ta yanke, inda ta soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta bai wa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC.

Jam’iyyar NNPP ta ce za ta daukaka kara zuwa kotu ta gaba, saboda rashin gamsuwa da hukuncin.

Bayan fitowa daga kotun, lauyan Jam’iyyar NNPP, Bashir Muhammad Tudun Wuzirci ya ce hukuncin ya zo musu da mamaki, domin bai kamata a ce an yi haka ba.

Lauyan ya ce NNPP za ta daukaka kara zuwa kotu ta gaba domin ba su gamsu da hukuncin ba.

Barista Bashir ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar cewa Kotun Daukaka Kara za ta warware abin da ya kira “Surkullen da aka yi wanda bai kamata a yi ba.”

Baritsa Tudun Wuzirci ya ce kafin tafiya kotu na gaba za su tattauna da wadanda yake wakilta domin daukar matakin da ya dace.

Ra’ayoyin Kanawa sun bambanta

Bayan bayyana hukuncin kotun wakilianmu sun tuntubi wasu magoya bayan Jam’iyyun APC da NNPP, inda A’isha Ahmad wata matar aure a Kano ta ce sun yi murna da wannan hukunci domin nasu ya samu

“A gaskiya mun ji dadin wannan hukunci domin dama tun farko Gawuna ne ya ci zaben amma saboda wasu dalilai na son zuciya aka ki bayyana shi a matsayin Gwamna. Yanzu alhamdulillah abu ya dawo hannunmu,” in ji ta.

Shi kuwa Nuhu Ahmad wani dan Jam’iyyar NNPP ya ce ba su ji dadin hukuncin ba.

Ya ce, “Gaskiya ba mu ji dadin wannan hukunci ba, duba da cewa hakan ya nuna ba dimokuradiyya ake yi a kasar nan ba, domin al’umma sun zabi gwamnatin da suke so amma ana kokarin hana su.

Ta yaya za a ce a lokacin kuna kan mulki da kanku kuka dauki mulkin nan kuka bayar amma sai daga baya ku zo ku ce ba ku yarda ba saboda an shirya wata kullalliya.

Kuma muna sanar musu cewa su daina murna in sha Allah sai mulkinmu ya dawo hannunmu.”

Wani dan Jam’iyyar APC ya nuna farin cikinsa inda ya ce suna maraba da gwamnati mai tausayin talakawa.

Ya ce, “Dama mu tun farko Gawuna muka zaba, amma aka yi mana magudi. Sai ga shi Allah Ya dawo mana da mulkinmu. Mun tabbatar maka Gawuna zai taimaki talakawa ‘yan kasuwa don haka muna yi masa maraba.”

Malama Zainab Bashir ’yar Jam’iyyar NNPP ce a Kano, ta bayyana hukuncin a matsayin “Wani abu na karfa-karfa da hadin baki daga Gwamnatin Tarayya domin ganin an kwace zaben daga wurin Abba.

“Duk mai bibiyar abubuwan da suke faruwa a siyasar Kano ya san Abba shi ne zabin talakawa.

“Wannan fa abin sun yi mana shi a 2019. Amma muna rokon Allah Ya ba mu nasara a kotun gaba,” in ji ta.

 

Daga Muhammad Aminu Ahmad, Abuja da Sani Ibrahim Paki, Kano

%d bloggers like this: