✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilan da ke jawo mutuwar aure’

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Kabiru Kauru ya bayyana rashin bin tsare-tsare da tanade-tanaden addinin Musulunci a matsayin dalilan da suke jawo mutuwar aure a Nijeriya…

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Kabiru Kauru ya bayyana rashin bin tsare-tsare da tanade-tanaden addinin Musulunci a matsayin dalilan da suke jawo mutuwar aure a Nijeriya da dama duniya baki daya.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lakca a wa’azin da Kungiyar Izala ta Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ta shirya a unguwar Hayin Banki Kaduna.

Malamin ya bayyana cewa, yana da kyau komai za a yi, a fara da tsarin Allah.

“Tsakaninku da Allah, wane ne da yake neman matarsa ya fara yin istikhara?

“Sannan idan an yi auren ko da saki za a yi, ana bin yadda Alla Ya tsara?”

Malamin ya ce, lallai idan ana son komai ya dawo daidai, dole a koma yadda tsarin Allah yake, sannan a samu sauki.

A nasa jawabin, Doka Nura Zubairu Dembo na Jami’ar Jihar Kaduna a nasa lakcar, ya mayar da hankali ne a kan wasiyyar da wani dalibin shehun malami Ibn Taimiyya, inda ya tambayi malamin ya masa wasiyya, inda shi kuma ya ce babu wata wasiyya da zai masa da ta wuce wasiyyar Allah ga bayinSa, wato jin tsoron Allah.

Daga cikin manyan baki a wajen wa’azin akwai Shugaban Agajin JIBWIS na Kasa, Dokta Mustapha Imam Sitti, da Shugaban JIBWIS na Kaduna, Sheikh Adamu Ibrahim da Shugaban Majalisar Malamai na Kaduna, Sheikh Aliyu da Sarkin Hayin Banki Malam Mahmud Shehu Galadima da shugabannin Kungiyar JIBIWS na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da na Unguwar Hayin Banki masu masaukin baki karkashin jagorancin Alhaji Gambo Lawal da limamin Masallacin Juma’a na Hayin Banki Sheikh Ishaq Ibrahim da sauransu.