✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilan da Jihar Kaduna ta kara kudin makaranta —Kwamishinan Ilimi

Ma'aikatar Ilimin Jihar Kaduna ta fayyace dalilan karin kudin makarantu.

A hira da manema labarai da aka yi da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Dokta Shehu Usman, ya yi karin bayani a kan dalilan da suka sa gwamnatin jihar ta yi karin kudin makaranta a manyan makarantun jihar, kamar haka:

Akwai rade-radin cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin kudin makaranta a manyan makarantun jihar, shin wasu nasarori ko koma-baya kuka samu a fannin ilimi har kuke ganin ya kamata ku kara kudin makaranta?

Da zuwan Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i abubuwa da dama suka canja a harkar ilimi, ya zo da sababbin canje-canje.

Da farko fannin ilimi ya fara samun kaso mafi tsoka a kasafin kudi fiye da yadda aka amince a taronsu na Abuja.

Na biyu, ya sanya fannin ilimi a shirin ko-ta-kwana (emergency), inda aka rika aikin gyara makarantu da yin sababbin gine-gine, da yin kujerun zama, aka rika girka abinci don ciyar da dalibai har aka zo matsayin da aka kara kudin da ake sayen littattafai.

Aka kara kudin da ake kashewa kan ciyar da dalibai a makarantun kwana.

Misalin da nake bayarwa koyaushe shi ne a yanzu ana kashe kusan Naira miliyan 800 wajen ciyar da dalibai.

A can baya ana karbar Naira 7,500, amma yanzu ba mu karbar ko kwabo kuma yanzu wannan kudin zai zo ya ninka saboda burin da gwamnatin ke da shi na kara yawan makarantun kwana.

Sannan ana kashe kudi masu yawan gaske wurin biyan malamai.

Mutane na sane kwanan nan muka tallata za mu dauki malaman sakandare 7,600 an yi musu jarrabawa, an gama tantance su domin mu samu mu inganta tsarin karantarwa.

Mun sani cewa a baya an yi ta kuka cewa wannan gwamnati ta kori ma’aikata 21,000 amma an manta mun dauki kwararrun malamai 25,000 da suka maye gurbin wadancan.

Mun kara yawan makarantu a jihar, yanzu haka a bana za mu bude sababbin makarantu shida da ake ginawa, a Pambeguwa da Jere da Rigachikun da Buruku da Manchok.

Sannan muna gina makaranta ta musamman ta zakakuran daliban Jihar Kaduna (Gifted and Talented), a nan Dan Bushiya.

Kuma muna kara yawan makarantunmu zuwa lungu da sakon jihar.

Yanzu haka muna da manyan makarantun 541 a Jihar Kaduna, ban da makarantun firamare sama da 4,000.

Wadannan nasarori da Malam Nasir El-Rufa’i ya samu a wannan dan lokaci ya faru ne saboda irin tunanin da yake da shi na cewa ilimi ne kadai zai iya inganta rayuwar al’umma ya kai su tudun-mun-tsira.

Shi ya sa kayan karatu da na makaranta da na karantarwa na kimiyya da fasaha koyaushe suna cikin kasafin kudinmu kuma shekara ba ta taba wucewa ba mu samu kudin nan mun kashe su kan wadannan abubuwa ba.

A takaice ina tabbatar muku wannan gwamnati ta cimma wani zango mai nisa a cikin wannan tafiya musamman da ta mayar da karatun firamare zuwa sakandare kyauta kuma dole a Jihar Kaduna.

Yanzu haka a firamarenmu muna da sama da dalibai miliyan daya da dubu 900 wadanda suke zuwa makarantun firamare da nazari na gwamnati.

Muna da dalibai sama da dubu 600 a makarantun sakandare; dalibai sama da dubu 20 da suke Jami’ar Jihar Kaduna (KASU); dubu 14 a Kwalejin Ilimi na Gidan Waya.

Akwai dalibai sama da dubu 12 da suke Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Nuhu Bamalli. Muna dalibai dubu biyar da 500 da suke Kwalejin Lafiya ta Shehu Idris. Muna da dalibai 1,560 da ke Kwalejin Ungozoma da ke nan Kaduna.

Sannan muna da dalibai sama da dubu 400 da suke makarantun masu zaman kansu.

Ka ga in ka kalli yawan daliban da ke zuwa makaranta a Jihar Kaduna, al’umma ce mai yawan gaske kuma hakkin kula da su yana kan Gwamnatin Jihar Kaduna.

An cimma zango mai nisa kuma gwamnati a shirye take ta ci gaba.

Abin da kawai zan kara shi ne duk wanda ya zagaya makarantunmu tun daga Kwalejin Kiwon Lafiya ta Makarfi zuwa Kwalejin Ungozoma, zuwa KASU inda ake gine-gine na mazaunin makarantar na dindindin zai ga irin yadda ake nutsar da kudi. Haka in ka zagaya sauran makarantunmu.

Mutum in yana so ya gani zai iya zuwa makarantunmu ya je G.G. Kawo da Kwalejin Rimi da sauransu ya ga irin ayyukan da muke yi.

Haka in mutum na so zai iya zagayawa makarantunmu na firamare, kwanan nan ma ba a yi ko mako biyu ba muka tura sama da ’yan kwangiloli 400 domin gina karin ajujuwa a makarantunmu na firamare.

Haka nan ba da dadewa ba za mu bayar da wasu ayyukan na kara gina kananan makarantun sakandare 90.

Za mu kara fadada makarantun sakandare ke nan da kimanin makarantu 80.

Wannan duk yana cikin burin wannan gwamnati na bunkasa ilimi a Jihar Kaduna.

Jama’a na ta korafin ko dan talaka zai iya karatu, la’akari da karin kudin makaranta da kuka yi a manyan makarantun, me za ka ce?

Maganar gaskiya ita ce gwamnati ba za ta iya bayar da ilimi tun daga matakin firamare har zuwa jami’a kyauta ba. Ba zai yiwu ba.

Kwanan nan Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya yi magana da al’ummar Jihar Kaduna yana fada musu idan suka je Abuja karbo kason kudin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya wani lokacin Naira biliyan biyar da miliyan 600, wani lokacin da miliyan 800, wani lokacin kasa da haka.

Amma abin da gwamnati ke biya a albashi kadai ya zarce Naira biliyan biyar da miliyan 300.

To idan ka yi lissafi za ka ga abin da ya rage maka bai isa ka yi cefane ba, musamman cefanen da ake yi a sauran ma’aikatun gwamnati na kayan aiki da sauran bukatunsu na yau da kullum da sauransu balle kuma a ce za a biya ’yan fansho da garatuti.

Abin da muke so mu yi bayani shi ne a takaice wajibi ne kai ma ka bayar da gudunmawarka a matsayinka na dan kasa.

Idan danka an ba shi ilimin firamare da na sakandare kyauta, to in za shi sama kai kuma sai ka bayar da taka gudunmawar.

Shi ake yi a ko’ina cikin kasar nan, shi ne muka ga mu ma ya kamata mu yi haka.

Kuma ko da gwamnati ta ce za ta yi hakan ba za ta iya ba, domin ba ta da kudin da za ta iya yin hakan.

Shin wannan dalilin ne ya sa kuka kara kudin makaranta a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) daga Naira dubu 26 zuwa Naira dubu 150?

Ai dama kudin makarantar Jami’ar Kaduna ba Naira dubu 26 ba ne. Tun shekarar 2005, Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna ta tsara za ta karbi kudin makaranta na Naira dubu 60 da wani abu.

A Gwamnatin da take ci a wancan lokaci ta ce mata a’a, ku karbi Naira dubu 26 da ’yan kai, mu kuma za mu cika muku sauran.

Kuma sun cika musu a wancan shekarar, haka da shekara ta dawo sun cika musu.

Amma daga nan ba su kara biya ba, aka fara mi’ara-koma-baya, suka zo ba su biyan su ko kwabo sai dai su karbi wannan kudi daga hannun dalibai su ci gaba da gudanar da jami’a.

Babban abin da suka rika yi a wancan lokaci ba zan ce suka yi ta yaudarar kansu ba, suna yi kamar za su iya suna daddagewa har suka zo yanzu gazawar ta bayyana.

Suka tabbatar ba za su iya gudanar da jami’a da wannan kudi ba.

Kudin nan in sun karba ba wai kudi ne da za su sa aljihunsu ba, kudi ne da za su biya albashi.

To kudin nan in sun tattara shi na shekara baki daya ba ya isa su biya albashin wata biyu na malaman Jami’ar KASU. To ina za a samo sauran? Saboda haka a koma wancan tsarin.

Ina son masu wannan tambayar su sani suna kallon KASU a matsayin wata makaranta ce da ya kamata su yi kyauta.

Amma akwai makarantun da na gwammati ne a Jihar Kaduna amma sun fi KASU tsada.

Mu je makarantunmu na Ungozoma da na jinya da suke karbar Naira dubu 80 a matsayin kudin makaranta kuma karatun da suke yi bai kai matsayin digiri ba.

Sannan ina so mutane su sani makarantarmu ta kiwon lafiya ta Makarfi babu wani dalibin da ke biyan kudin makaranta kasa da Naira dubu 50, amma Jami’ar KASU ana karbar Naira dubu 26.

To so ake yi sai Jami’ar KASU ta durkushe ta yadda kowa zai dauki dansa ya kai Kano ko Maleysiya ko Sudan?

Haka ake so mu ci gaba da gudanar da Jami’ar KASU har sai ta durkusa?

Ai wannan ba zai yiwu ba, shi ya sa Allah Ya ba wadansu jagoranci saboda su yi abin da ya dace.

Bugu da kari ina so mu sani a lokacin da wannan dalibi yake Jami’ar KASU yana biyan Naira dubu 26, shi kuma a daya bangaren ya karbo sama da Naira dubu 100 a matsayin tallafin karatu a wurin gwamnati.

Saboda haka ba zai yiwu mu kara kudin tallafin karatu daga Naira dubu 10 ko dubu 20 ba, mu mayar da shi Naira dubu 100 amma kudin makaranta yana Naira dubu 26 ba.

Muna so mu bayar da ilimi mai inganci. Muna so Jami’ar KASU ta tsaya da kafafunta ce.

Muna so mu bayar da ilimin da kowa zai rika yabawa har wani ya yi sha’awar kawo dansa.

Haka kuma in muka dauki makarantar da ke koyon aikin jinya da ke nan Kaduna, ta Gwamnatin Jihar Kaduna ce suna karbar Naira dubu 80 da wani abu ne.

Kwanakin baya suka yi talla za su dauki dalibai masu koyon karatun jinya.

Sun samu masu bukatar shiga karatun sama da mutum dubu 50. Kuma gurbi 50 hamsin kacal suke da shi, idan sun yi kokari shi ne su dauki mutum 100 daga baya a rika tafiyar yada-kanin-wani, har a tsaya a 50 din.

To, don me za mu rika yaudarar kanmu?

Ba gara mu karbi abin da ya kamata su karba ba su kara kayan aikinsu da wuraren karatu, su kara yawan malamai da na’urorin da suke bukata domin hukumar da ke kula da su, su zo su ce yanzu mun kara muku yawan daga 50 zuwa 100 ko 200 ba?

Ita kanta KASU wadanda suka nemi shiga bangaren likitanci ko harhada magunguna suna da gurbin mutum 200 misali, amma suna da dubban dalibai da suka nemi shiga kuma sun cancanta su shiga makarantar amma gurbin da aka ba KASU na daukar daliban ba zai isa ba.

Ka ga da suna da kudi da sun fadada sun dauki sama da 200. Wannan shi ne dalilinmu, muna fata jama’a za su fahimce mu.

Da Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya da Makarantar Kiwon Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi da ta Pambegua da ta nan Kaduna, an ba su dama, gwamnati ta fadi mafi karancin abin da ya kamata su caza; jami’a kada ya zama kasa da Naira dubu 150.

Su za su zauna su duba nawa ne wanda zai dawo yake shekarar karatu na biyu ko na uku zai biya.

Nawa ne mazaunin Jihar Kaduna zai biya, nawa ne wanda ba mazaunin Jihar Kaduna ba zai biya?

Nawa ne mai kimiyya zai biya, nawa ne mai fasaha zai biya. Nawa ne mai karatun likitanci zai biya, wannan an tura musu.

Haka sauran makarantu su ma an yanke musu; masu karatun diploma za su biya Naira dubu 70, kuma dama abin da suke biya kamar hakan ne. Wadansu ma fiye da haka suke biya.

Sannan babbar diploma Naira dubu 100, dama haka suke biya, wanda bai sani ba ne yake tunanin an kara zuwa sama.

Sannan da muka ce su karbi wannan kudi, sai kuma muka hana karbar duk wasu kudade domin da in an karbi wannan kudi daga baya kuma sai a ce je ka kawo kudin takarda, je ka kawo kudin fartanya, je ka kawo kudin sinadari kaza da sauransu.

Sai muka ce in aka karbi wancan kudi, to kada a kara karbar wani kudi.

To, wannan ne muke so mutane su gane kuma da yawa sun gane dalilinmu na yin haka.

Saboda dalibai sukan fake da wannan suna karbar kudi a wurin iyayensu su ce a kawo kudin liman, su ce a kawo kudin ladan, su ce a kawo kudin shugaba (Bice Chancellor, Rector da Probost). Wannan duk karya ce.

Wannan dalilin ya sa muka ce duk a hade kudin wuri daya. Ba za a sake rabawa ba, balle wani ya samu damar da zai je ya yi karya ya ce an ce ya kawo kudin sashi ‘department’ ko na amincewa ‘acceptance,’ duk an soke wannan yanzu.

Kuma ina fata wadanda suka san kimar ilimi za su taimake mu wurin bayani saboda da yawa wadanda suka san kimar ilimi sun dauki ‘ya’yansu sun kai su makarantu masu zaman kansu, sun dauki ’ya’yansu sun kai makarantu a kasashen waje saboda sun san kimar ilimi.

Amma abin takaici abin haushi, irin wadannan su ke zuga talaka da ke kauye kada ya yarda cewa sai ya sayar da gonarsa dansa ya yi ilimi, amma shi ba mu san abin da ya sayar ba ya kai ’ya’yansa Maleysiya ko ya tura su Sudan ko Masar ko Amurka ko Ingila ba.

A karshe muna fada wa al’ummar Jihar Kaduna cewa, Hukumar Bayar da Tallafin Karatu, ta yi tsari tana bayar da tallafin karatu.

Kuma ‘scholarship’ din nan an kara yawan kudin daga Naira dubu 15 ko dubu 20 zuwa sama da Naira dubu 100. A baya abin ba haka yake ba.

Sannan in ba ka samu wannan ba, an yi wani tsari da dalibi zai iya karbar bashi wanda ba ya da wani ruwa a cikinsa, mutum ya yi karatunsa in ya gama ya biya.

Tuntuni ake irin wannan tsarin a kasashen duniya, kuma yanzu an yi tsarin da ba ka bukatar sai ka je wani ofishi sannan ka nemi wannan tallafin karatun.

Kana zaune a cikin dakinka za ka shiga intanet ka sanya duk bayananka domin neman wannan tallafi.

Muna fata al’umma za su yi amfani da wannan dama domin su nemi wannan tallafi su biya wa ’ya’yansu kudin makaranta.

Wanda bai da hali shi ake ba wannan tallafi, wanda kuma yake da hali akwai nasa tsarin na musamman.

Saboda haka ya kamata a yarda gwamnati ta yi iya yin ta, ta dauki tsawon zamani tana yin wannan kuma mun fahimci in ba a yi wannan tsari ba makarantunmu za su durkushe. Ilimin zai durkushe gaba daya.

Kuma ba zai yiwu a yi karya za a yi wani abu ba, kuma a kasa yi ba.

Abin da aka ce za a yi, kuma za mu iya, shi ne ilimin firamare zuwa sakandare kyauta, kuma za mu yi iya kokarinmu mu ga iyaye ba su bayar da ko kwabo ba sai dai wanda ya ga dama ta hanyar PTA.

Abu na biyu duk wanda ya san kimar ilimi ya san bai taba tsada ba, musamman in aka kwatanta shi da jahilci.

Na uku, mu sani in muka ce za mu yaudari kanmu mu ci gaba da zama a halin da muke ciki, wadanda suke da hali za su ci gaba da kwashe ’ya’yansu suna kai wa makarantu masu zaman kansu da kasashen waje, dan talaka kuma ya sha wuya.

Shi ya sa muka ga gara a kara wannan kudi dan talaka ya samu ingantaccen ilimi a gida, maimakon komai ya tabarbare ya koma yana neman jami’a mai zaman kanta yana biyan Naira miliyan daya ko miliyan biyu.

Muna tabbatar wa jama’a wadannan kudade da aka kara za a yi amfani da su wurin inganta ilimi a jami’o’i da makarantunmu, a dauki malamai a biya su hakkokinsu kamar yadda ya kamata.

Mun kafa kwamiti su bincika mana hakikanin nawa ya kamata a kashe wa kowane dalibi, sannan sai mu ga nawa za mu rika bayar da tallafi domin kowane dalibi ya samu ingantaccen ilimi.

Abdullah Yunus [email protected]

%d bloggers like this: