✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Dalilai 7 da za su sa Majalisar Dinkin Duniya ta amince da Ranar Hausa a hukumance’

Ya ce dalilan guda bakwai sun isa su sa MDD ta amince da ranar.

A yayin da ake ci gaba da bikin Ranar Hausa ta Duniya na bana, wani Shehin malami kuma Farfesa a fannin adabin Hausa, Farfesa Abdulkadir Dangambo, ya ce akwai dalilai da dama da ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta yi la’akari da su wajen ayyana ranar 26 ga watan Agusta a matsayin ranar Hausa a hukumance.

Farfesa Dangambo, wanda malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawarsa da Aminiya.

A cewarsa, karan yaren ya kai tsaikon da za ta ware masa rana a hukumance, kamar yadda ta yi wa wasu yarukan, musamman la’akari da yawan masu amfani da shi a fadin duniya.

Ga kadan daga cikin dalilan da Farfesan ya zayyano:

  1. Na farko a kwai yaruka kimanin 6,500 a duniya, kuma Hausa ce ta 11 a jerin wadanda aka fi amfani da su daga cikin wannan adadin. Ko da yake ni ina jin adadin ma zai wuce haka matuka, kasancewar akwai mutane sama da miliyan 200 a Najeriya kawai, kuma fiye da rabinsu suna jin Hausa.
  2. Na biyu, ana amfani da yaren, ba wai kawai a yankin Afirka ta Yamma ba, a’a, akwai masu amfani da yaren da suka war-watsu a kasashe fiye da 30.
  3. Kazalika, Hausa ne yare mafi girma a Nahiyar Afirka, sama ma da harshe Swahili.
  4. Bugu da kari, akwai manyan makarantu da dama a sassa daban-daban na duniya da ke koyar da Hausa a matsayin yare, ciki har da na kasashen Turai da Amurka da nahiyar Asiya.
  5. Sannan akwai bangaren karbuwa da yin fice. Yanzu haka bincike ya nuna cewa akwai gidajen rediyo sama da 400 da suke watsa shirye-shirye da harshen na Hausa, ciki har da a kasashe kamar su Ingila da Amurka da Rasha da China da Jamus da Faransa da Masar da Libya da dai sauransu.
  6. Akwai Jaridu akalla 150 a fadin duniya da ke wallafa labarai da harshen.
  7. Ta bangaren karatu kuwa, akwai, jami’o’i sama da 100 da suke bayar da shaidar digiri a Hausa a fadin duniya, yayin da adadin masu akalla digirin farko ya haura 100,000.