A yayin da ake ci gaba da bikin Ranar Hausa ta Duniya na bana, wani Shehin malami kuma Farfesa a fannin adabin Hausa, Farfesa Abdulkadir Dangambo, ya ce akwai dalilai da dama da ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta yi la’akari da su wajen ayyana ranar 26 ga watan Agusta a matsayin ranar Hausa a hukumance.
Farfesa Dangambo, wanda malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawarsa da Aminiya.
A cewarsa, karan yaren ya kai tsaikon da za ta ware masa rana a hukumance, kamar yadda ta yi wa wasu yarukan, musamman la’akari da yawan masu amfani da shi a fadin duniya.
Ga kadan daga cikin dalilan da Farfesan ya zayyano:
- Na farko a kwai yaruka kimanin 6,500 a duniya, kuma Hausa ce ta 11 a jerin wadanda aka fi amfani da su daga cikin wannan adadin. Ko da yake ni ina jin adadin ma zai wuce haka matuka, kasancewar akwai mutane sama da miliyan 200 a Najeriya kawai, kuma fiye da rabinsu suna jin Hausa.
- Na biyu, ana amfani da yaren, ba wai kawai a yankin Afirka ta Yamma ba, a’a, akwai masu amfani da yaren da suka war-watsu a kasashe fiye da 30.
- Kazalika, Hausa ne yare mafi girma a Nahiyar Afirka, sama ma da harshe Swahili.
- Bugu da kari, akwai manyan makarantu da dama a sassa daban-daban na duniya da ke koyar da Hausa a matsayin yare, ciki har da na kasashen Turai da Amurka da nahiyar Asiya.
- Sannan akwai bangaren karbuwa da yin fice. Yanzu haka bincike ya nuna cewa akwai gidajen rediyo sama da 400 da suke watsa shirye-shirye da harshen na Hausa, ciki har da a kasashe kamar su Ingila da Amurka da Rasha da China da Jamus da Faransa da Masar da Libya da dai sauransu.
- Akwai Jaridu akalla 150 a fadin duniya da ke wallafa labarai da harshen.
- Ta bangaren karatu kuwa, akwai, jami’o’i sama da 100 da suke bayar da shaidar digiri a Hausa a fadin duniya, yayin da adadin masu akalla digirin farko ya haura 100,000.