✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliget: Shugaban APC na Nasarawa da na Kasa sun sa Zare

Sabon rikici ya barke a jam’iyar APC Reshen Jihar Nasarawa kan zargin sauya sunayen daliget a wasu kananan hukumomin jihar da uwar jam’iyar ta yi,…

Sabon rikici ya barke a jam’iyar APC Reshen Jihar Nasarawa kan zargin sauya sunayen daliget a wasu kananan hukumomin jihar da uwar jam’iyar ta yi, karkashin shugabanta na kasa Abdullahi Adamu.

Da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyar a Lafia a daren ranar Alhamis, Mamman ya ce sun janye daga zaben fidda gwanin saboda an maye gurbin sunayen daliget din da suka mika da wasu da ba su sani ba.

“Dole mu janye daga zabukan fidda gwanin har sai an yi gyara kan wannan maganar”, in ji shi.

“Wannan abu da Adamu ya yi ya saba wa Dimokuradiya, domin zai haifar da rabuwar kai a jam’iya, don haka ba za mu taba amincewa da sunayen wadannan daliget ba”, in ji shugaban APC na Nassarawa.

Ya kuma ce suna bakin ciki da yadda shugabncin jam’iyar na kasa ya yi watsi da sunayen daliget din suka tura Sakatariyar APCn ta Kasa, in da ta maye gurbinsu da sabbi a kananan hukumomin jihar da dama.