Sabon rikici ya barke a jam’iyar APC Reshen Jihar Nasarawa kan zargin sauya sunayen daliget a wasu kananan hukumomin jihar da uwar jam’iyar ta yi, karkashin shugabanta na kasa Abdullahi Adamu.
Da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyar a Lafia a daren ranar Alhamis, Mamman ya ce sun janye daga zaben fidda gwanin saboda an maye gurbin sunayen daliget din da suka mika da wasu da ba su sani ba.
- Ranar yara: Waje 6 da ya kamata yara su ziyarta don shakatawa
- Talakawa ba za su shiga Aljanna ba – Ministan Uganda
“Dole mu janye daga zabukan fidda gwanin har sai an yi gyara kan wannan maganar”, in ji shi.
“Wannan abu da Adamu ya yi ya saba wa Dimokuradiya, domin zai haifar da rabuwar kai a jam’iya, don haka ba za mu taba amincewa da sunayen wadannan daliget ba”, in ji shugaban APC na Nassarawa.
Ya kuma ce suna bakin ciki da yadda shugabncin jam’iyar na kasa ya yi watsi da sunayen daliget din suka tura Sakatariyar APCn ta Kasa, in da ta maye gurbinsu da sabbi a kananan hukumomin jihar da dama.