✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibin SS 1 ya rataye kansa saboda faduwa jarrabawa

Wani dalibin aji daya a babbar sakandare (SS I) mai suna Adegoke Adeyemi da ke yankin Karamar Hukumar Offa a Jihar Kwara, ya kashe kansa…

Wani dalibin aji daya a babbar sakandare (SS I) mai suna Adegoke Adeyemi da ke yankin Karamar Hukumar Offa a Jihar Kwara, ya kashe kansa saboda faduwa jarrabawa.

Ana zargin marigayin ya kashe kansa ne saboda rashin cin jarrabawar da za ta ba shi damar shiga aji na biyu a matakin babbar sakandare (SS2).

Bayanan Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ranar Laraba a Ilorin, sun nuna marigayin ya ji kunyar maimaita SS1 da aka ce ya yi shi ya sa ya gwammace ya kashe kansa.

Jami’in ya ce marigayin wanda dan shekara 17 ne, ana kyautata zaton ya kashe kansa ne ta hanyar rataya bayan da ta tabbata gare shi cewa ya fadi jarrabawar.

“Jami’anmu na Ofishin ’yan sanda da ke Offa, sun sami rahoto da misalin karfe 15:34 a ranar 2/8/2022, cewa an ga wani yaro rataye babu rai a jikin wata bishiya a bayan wani otel. Ba tare da bata lokaci ba aka tura tawagar ‘yan sanda wurin,” inji jami’in.

Ya kara da cewa, bayan sauke gawar a ranar Talata da misalin karfe 03:34, an dauke ta zuwa Babban Asibitin Offa don gwaji yayin da kuma aka kaddamar da bincike a kan batun.