Wani dalibin aji daya a karamar sakandare (JSS 1) a da ke Maiduguri, ya kirkiro wani karamin injin janareta mai ba da hasken wutar lantarki da sam ba ya amfani da man fetur.
Muhamma Kaumi Bashir, dalibin makarantar Al-Ansar Academy ya kirkiro janaretan ne da ke iya kunna fitulu a gidansu ba tare da tallafin kowace na’ura ba face wacce ke jikinsa.
- An kama fasto da dansa kan zargin daddatsa buduruwa a cocin Abuja
- Yan bindiga sun sace matar soja da wasu mutum 6 a Kaduna
Wata Majiya ta bayyana cewa, dalibin mai shekara 11, a cikin faifan bidiyo na kasa da minti biyu da manema labarai suka samu, an gan shi yana ‘gwajin’ na’urar wutar lantarki da ya ‘kirkiro’.
A cewar mahaifiyar Bashir, Malama Yakaka Kaumi, danta ya fara nuna fasaharsa ta kere-kere ce tun yana dan shekara biyar.
“Ya zuwa yanzu rayuwarsa ta kasance game da kirkira da gyara na’urorin lantarki,” inji ta.
Malama Kaumi, ta ce danta ya dade yana mafarkin zama mashahurin injiniyan lantarki nan gaba kamar yadda ya ke ambata mata a kullum.
Ta kara da cewa: “Yakan tashi kowace rana ya gaya mini cewa yana son ya zama mashahurin injiniyan lantarki, wanda za a san shi a duk duniya.
“Yana da sha’awar kafa wani babban kamfanin injiniyan lantarki, sannan ya yi amfani da shi wajen magance matsalar wutar lantarki a kasar nan da ke shirin gagarar kwandila.”
Don haka Mahaifiyar Bashir ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Borno, da Gwamnatin Tarayya, tare da ’yan uwa masu kokari da su taimaka wa danta ya cim ma burin nasa ‘dauwamamme’.
A nasa bangaren, yaron mai kirkirar ya shaida wa Aminiya cewa burinsa shi ne ya zama injiniyan lantarki wanda zai taimaka wajen magance matsalar wutar da Najeriya ta kwashe shekaru masu yawa tana fama da ita.
Bashir ya ce ya kirkiri janareta ne domin samar da haske ga gidansu.
Ya ce tun da garin su na Maiduguri ya shafe sama da shekara biyu yana fama da matsalar wutar lantarki, kuma mahaifinsa ba zai iya saka hasken rana ba, sai ya yanke shawarar kera wannan janareta da ba ya amfani da man fetur, kuma zai iya ba da hasken wutar lantarki a gidansu.
Kamar yadda Aminiya ta gano cewa kayayyakin da Bashir ya yi amfani da su wajen kera karamin janaretan sun hada da capacitors guda biyu, waya, fitulu, kugiya ta karfe da fanka, da dai sauransu.